1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'addanci ya mamaye jawabin Merkel na shiga 2017

December 31, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi wa 'yan kasa jawabin shiga 2017, inda baya ga al'amuran EU da zaben da ke tafe a kasar ta bukaci Jamusawa su jajirce dangane da hare-haren ta'addaci da kasar ke fama da su.

https://p.dw.com/p/2V5aZ
Deustchland | Neujahrsansprache BK Merkel im Bundeskanzleramt
Hoto: REUTERS/M. Schreiber

Angela Merkel ta danganta 2016 a matsayin shekarar da ke cike da kalubalen tsaro ga kasar Jamus. Wannan kuwa ba ya rasa nasba da jerin hare-haren ta'addanci da kasar ta fuskanta a biranen Würzburg da Ansbach da kuma Berlin a baya-bayannan.  Sai dai kuma shugabar gwamnatin Jamus ta ce ayyukan na ta'addanci ba za su hana Jamus ci gaba da bayar da mafaka ga wadanda ke gudun yaki a kasar Syriya kamar yadda kundin tsarin mukin kasar ya tanada ba.

"Idan muka ci gaba da gudanar da rayuwarmu da aikinmu yadda muka saba, muna gaya wa 'yan ta'adda ne cewar sune kiyeyya ke sa kashe-kashe, amma ba zai samu canza salon rayuwa ba. Mu mutane ne masu 'yanci da tariyar baki. Idan aka yi misali da halin ake ciki a Syriya, za a fahimci muhimmancin matakin da kasarmu ta dauka a shekarar da ta gabata na bude kofa ga 'yan gudun hijira tare da rungumarsu hannu biyu."

Al-Hamza Family
'Yan gudun hijira sun rada wa 'yarsu sunan Angela MerkelHoto: DW/R. Jarmakani

Angela Merkel ta yi alkawarin daukan karin matakan tsaro a 2017 domin kare rayuku da dukiyoyin Jamusawa daga hare-hare, inda cikin jawabin nata ta ce wannan zai samu ne ta hanyar hadin kai da taimakon juna tsakanin kasashen Turai baki dayansu. Ita dai shugabar gwamnatin Jamus ta na tsokaci ne game da kada kuri'ar fita daga cikin Kungiyar Gamayyar Turai da 'yan Birtaniya suka yi.

"Tabbas, al'amuran Turai na tafiyar hawainiya. Amma dole ne mu dauki matakan raba gari da daya daga cikin membobinmu cikin ruwan sanyi. Ya kamata Turai ta mayar da hankali kan abin da zai iya zame mata alhairi maimakon son kai da kasa daya ke nunawa. Mu Jamusawa kada mu taba yarda da irin wannan rudi , domin ba za mu samu makoma na gari ba idan muka mayar da kanmu saniyar ware."

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta na nuna damuwa ne dangane da karbuwa da jam'iyyar AfD da ke kyamar baki da manufofin Turai ke yi a kasar, a daidai lokacin da ta bayyana aniyar tsaya takara a karo na hudu. A watan Satumba na 2017 ne za a gudanar da zaben 'yan majalisa na Bundestag. Idan za a iya tunawa dai jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta ja baya a zabukan da aka gudanar da wasu jihohi na Jamus, lamarin da ke nuna irin kalubalen da ke gabanta wajen samun kaso da zai bata damar yin tazarce.