1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 19.07.2017

Mohammad Nasiru Awal
July 21, 2017

Matsalar talauci na karuwa a Italiya saboda dalilai na matsin tattalin arziki musamman a kudancin kasar. Wannan matsalar ta fi shan iyalai masu 'ya'ya da yawa.

https://p.dw.com/p/2gydS

Kasar Italiya daya daga cikin manyan kasashen kungiyar tarayyar Turai EU. Sai dai duk da kasancewar kasar a sahun gaba na kasashen na EU, matsalar talauci na karuwa a kasar saboda dalilai na matsalar tattalin arziki musamman a kudancin kasar. Alkalumman da cibiyar kididdiga ta kasar Italiyar ta bayar sun nuna cewa kashi daya cikin uku na 'yan kasar na fuskantar barazana ta talauci, yayin da a kudancin kasar yawan ya kai kashi 50 cikin 100 wato mutum guda cikin mutum biyu. Iyalai masu 'ya'ya da yawa ke cikin hadarin fadawa cikin talauci a kasar ta Italiya