1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ba za ta sayar da wasu jiragen samanta

Ubale Musa/AHJune 19, 2015

Da farko Jaridu a Najeriya sun ce Muhammadu Buhari ya ba da umarnin sayar da jirage tara a cikin jiragen da ke ƙarƙashin offishinsa.To amma daga bisani Garba Shehu wani mashawarcin shugaban ya ce ba ya da labari.

https://p.dw.com/p/1Fjmr
Muhammadu Buhari steigt aus einem Flugzeug
Muhammadu Buhari na sauka daga cikin jirgin samaHoto: GettyImages/AFP/M. Safodien

A baya dai offishin na Shugaban ƙasa ka dai na taƙama da jirage kusan takwas na hawansa kowane lokaci, ban da kuma offishin mataimakin shugaban ƙasa da shugabannin majalisun tarrayar ƙasar biyu dama wasu ma'aikatu 'yan gata.

Sauyi a cikin al'amuran mulki a Najeriya

To sai dai kuma tana shirin sauyawa a cikin shugabanci na ƙasar inda sabon shugaban ya ba da umarnin cefanar da aƙalla tara a cikin jirage kusan 16 da ke zaman mallakin mahukunta na ƙasar.Ana dai sa ran samun dubban miliyoyi daga cinikin jiragen saman.Tuni dai da Buharin ya yi alaƙwari na cefanar da jiragen da ya ce na zaman ɓarna ta kuɗi ga ƙasar da talakawanta ke kiran ni 'yasu amma shugabanninta ke rayuwar masha'a.To sai dai kuma babban saƙo a tunanin Garba Umar kari da ke zaman manazarci a kan al'amura na ƙasarda ke kallon cewar wani a lamari ne da ke shirin kawo ƙarshen yin ɓarna da dukiyyar ƙasar

Passagierflugzeug in Nigeria abgestürzt
Hoto: AP

Ana kashe kaƙuden kuɗaɗe domin kula da jiragen

Aƙalla naira Miliyan dubu 12 ne dai ake kashewa a duk shekara wajen gyara da kuma tabbatar da jiragen na bisa tsari, ban da wasu miliyoyin da a kan kashe domin biyan haraji da kuɗaɗen ajiyarsu a ciki dama wajen ƙasar.Abin kuma da a cewar Dr Nazifi Darma da ke zaman masani na tattalin arziki ke iya biyan da dama a cikin na buƙatun al'umma yanzu.Abin jira a gani dai na zaman irin matakai na gaba ga gwamnatin da ke da ɗimbin aikin sauyi daga al'adar masha'ar da ta ɗauki lokaci tana cinye kuɗin ƙasar.To sai dai kuma daga bisani bayan fitar wannan rahoton wasu rahotannin sun ambato wani mashawarci a fadar shugaban ƙasar wato Garba Shehu yana mai cewar ba shi da masaniya a kan batun amma kuma bai ƙaryata labarin ba.

Nigeria Flughafen Katsina
Daya daga cikin filayen saukar jiragen sama na NajeriyaHoto: DW