Tababa game da ikirarin nasara a Mali
February 7, 2013Dakarun Faransa da ke yankin arewacin Mali na farautar 'yan tawayen da mai yiwuwa suka saje da al'ummar birnin Gao, bayan bata-kashin daya gudana kusa da birnin, wanda ya aza ayar tambaya game da ikirarin da Faransar ta yi na kwace iko da birnin.
Kakakin sojin Faransa a Mali Kanal, Thierry Burkhard ya fadi - a wanna Alhamis cewar, har yanzu suna gudanar da samamen kwace iko da birnin, furucin da kuma ke zuwa kimanin makonni biyu bayan da dakarun Faransa da na Mali suka shiga cikin birnin. Burkhard, ya fadi a birnin Paris na Faransa cewar, akwai hatsarin yiwuwar masu kaddamar da farmaki na cudanya da mazauna birnin na Gao.
A dai ranar Talatar da ta gabata ce wasu mahara suka harba makamai masu linzami akan sojojin Faransa kusa da birnin na Gao. Idan za'a iya tunawa dai a ranar 11 ga watan Janairu ne dakarun Faransa suka kaddamar da samame da nufin tallafawa sojojin Mali sake kwace iko da arewacin kasar, wanda masu kishin addini suka yi tsawon watanni tara suna gudanar da mulki a ciki.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas