1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tagwayen Hare hare a kasar Afghanistan

February 24, 2013

Mutane da dama sun rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da 'yan taliban suka kai a wasu sassa na gabashin Afghanistan da kuma Kabul babban birni.

https://p.dw.com/p/17kpK
Hoto: Reuters

Wasu hare haren kunar bakin wake da aka kaddamar a wannan lahadin a biranen Jalalabad da kuma Puli Alam da ke gabashin Afghanistan sun lamshe rayukan mutane akalla uku. Tuni dai 'yan taliban suka dauki alhakin wadannan tagawayen hare haren. Su dai masu kaifin kishin addini na Afghanistan sun saba amfani da wadannan hanyoyin wajen yakar gwamnatin Kaboul da kawayenta na NATO tun bayan da suka fatattake su daga kujerar mulki a karshen shekara ta 2001.

Majalisar Dinkin Duniya ta nunar cikin wani rahoto da ta fitar a ranar talata cewa hare-haren kunar bakin wake da masu tsattsauran ra'ayin addini ke gudanarwa sun ragu a watannin baya-bayannan. Rabon 'yan taliban su kai wani mummunan harin kunar bakin wake tun ranar 26 ga watan janairu a Kundunz da ke arewacin Afghanistan inda 'yan sanda goma suka rasa rayukansu yayin da wasu karin 18 suka jikata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar