1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tagwayen hare-hare a Nairobin Kenya

May 16, 2014

Mutane hudu sun mutu a babban birnin kasar Kenya sakamakon fashewar wasu abubuwa da ake dangantawa da bama-bamai .

https://p.dw.com/p/1C1KO
Hoto: Reuters

Daya daga cikin abubuwa da ake dangantawa da bama-baman dai ya tashi ne a kusa da wata kasuwa a Narobi, yayin a daya kuma ya fashe a cikin wani bus da ke dauke da fasinjoji. Hukumar bayar da agjin gaggawa ta kasar kenya ce ta wallafa wannan labari a shafinta na Twitter. Sai dai ya zuwa yanzu babu wasu sahihan bayanai da a a samu a kan musababbin tashin-tashinan ba.

Hare-haren ta'addancin na neman zama ruwan dare a kasar ta Kenya. A farkon wannan wata na mayu ma dai, wasu jerin hare-haren da aka kaddamar a Nairobi da kuma Mombassa sun yi awan gaba da rayukan mutane bakwai yayin da wasu sama da 100 suka samu raunuka.

Tun bayan da gwamnatin Kenya ta sa kafar wando guda da 'yan al-Shabab na Somaliya ne, wasu birane na kasar Kenya suka zama dandali na tashin bama-bamai.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu