Takaddama tsakanin Turkiyya da Amirka a kan rikicin Siriya

Now live
mintuna 02:20
Ganawa tsakanin John Bolton mai bada shawara kan harkokin tsaro ga shugaban Amirka da jami'an Turkiyya ta kasance takaitacciya. Sabani ya bayyana karara. Kakakin Erdogan shi ne ya tarbe shi, amma ba shugaban da kansa ba. Ankara ta ki amincewa da sakon da Bolton ya je da shi na manufar Amirka a Siriya.