1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin bil Adama a Kamaru

Yusuf BalaSeptember 17, 2015

Firsinoni 25 ne suka rasu yayin da mutane 130 suka bace a bangaren Boko Haram kuma ta halaka mutane kimanin 380 da yanka wasu 30.

https://p.dw.com/p/1GXhu
Nordkamerun Grenzregion zu Nigeria Soldaten Anti Terror
Dakaru a kan iyakar KamaruHoto: AFP/Getty Images

Kungiyar kare hakkin bal Adama ta Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike kan musabbabin rasuwar wasu firsinoni 25 da bacewar wasu mutane 130 bayan wasu ayyukan dakarun tsaron kasar Kamaru wani abu da ke nuna alamun yiwuwar take hakin bil Adam a yakin da kasar ke yi da mayakan Boko Haram.

Da take fitar da rahotonta a jiya Laraba kungiyar ta Amnesty ta ce mayakan na Boko Haram masu sansani a Najeriya sun aikata laifukan yaki a kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya inda suka hallaka akalla fararen hula 380 tun da ta fara aikinta a shekarar bara, inda a yayin wani farmaki da takai a watan Oktoba ta yanka makogwaron mutane 30 a garin Ambchide da ke a kan iyaka.

A cewar kungiyar ita ma da take nata aikin bada kariyar ga farararen hula rundinar sojan kasar ta Kamaru ta aikata manyan laifuka na take hakin bil Adama yayin kame mutane 1000 da ake zargi da kisan wasu fararen hula da lalata gine-gine a kauyikansu.

Mista Steve Cockburn mataimakin darakta a kungiyar ya ce ya zama dole mahukunta a kasar ta Kamaru su gudanar da bincike kan kisan 'yan baruwanmu da bacewar mutane da ma sake nazari kan wadanda aka garkame a gidan kaso.