1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka kan yarjejeniyar cinikayya ta TTIP

Mohammad Nasiru Awal/GATAugust 31, 2016

Yarjejeniyar cinikin maras shinge da ake shirin kullawa tsakanin Amirka da kasashen Tarayyar Turai wato TTIP na iya rage yawan kudaden da kamfanoni da sauran bangarorin tattalin arziki ke kashewa.

https://p.dw.com/p/1JtBC
TTIP Europa USA
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Hoslet

Tun shekaru uku da suka wuce kasar Amirka da kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ke tattaunawa kan kulla wata yarjejeniyar ciniki maras shinge da ake wa lakabi da TTIP. A karshen wannan shekara ake sa ran kammala tattaunawar tare kuma da sanya hannu kan yarjejeniyar, da ke shan suka da kakkausan lafazi. A halin da ake ciki kasashen Jamus da Faransa da ke sahun gaba wajen karfin tattalin arziki a Turai suna nuna shakku kan wanzuwar yarjejeniyar.

Yarjejeniyar cinikin maras shinge da ake shirin kullawa tsakanin Amirka da kasashen Tarayyar Turai wato TTIP ka iya rage yawan kudaden da kamfanoni da sauran bangarorin tattalin arziki ke kashewa, domin za ta kawar da kudin fito ko na kwastan tare kuma da daidaita harkokin cinikiya tsakanin sassan biyu. Sai dai yawan masu sukar yarjejeniyar na karuwa. A halin yanzu ministan tattalin arzikin Jamus Sigmar Gabriel ya sake jaddada adawarsa da yarjejeniyar ta TTIP. A ra'ayinsa matsayin Amirka na kin ba da hadin kai ne dalilin rashin cimma matsaya kan yarjejeniyar ta kawar da shingen ciniki:

Demo gegen CETA und TTIP in Brüssel
Hoto: picture alliance/dpa/O. Hoslet

"A ganina tattaunawar da muke yi da Amirka a fakaice ta ruguje, ko da yake ba wanda ya fito fili ya amince da haka. Kawo yanzu an yi zagaye 14 na tattaunawar a kan batutuwa 27, amma har yanzu babu wani abu takamaime da suka amince a kai. Ko da yake akwai wata tattaunawa da za a yi a watan Oktoba, amma ba na jin za a kammala ta kafin karshen wannan shekara."

Shi ma a lokacin da yake magana game da yarjejeniyar, Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce babu daidaito a tattaunawa kan kokarin cimma yarjejeniyar mai cike da tarihi tsakanin Amirka da EU, inda ya ce ba za a kammala ta kafin cikar wa'adin mulkin Shugaba Barack Obama ba:

"Tattaunawar da ake yi game da dangantakar ciniki da zuba jari wato TTIP ba za ta kai ga cimma yarjejeniya kafin karshen shekara ba. Shawarwarin sun cije ba a kuma martaba matsayin juna. Abu mafi kyau da ya kamata mu gane shi ne maimakon a ci gaba da wata tattaunawar da ba za a iya kammala ta kan kyakkyawar turba ba, ya kyautu mu bari kowa ya sani cewa Faransa ba za ta amince da wata yarjejeniyar da ba a tsara ta kan turba ta gaskiya ba."

Sai dai a nata bangaren gwamnatin Amirka a ta bakin mataimakiyar shugaba ta musamman a kan tattalin arzikiin kasa da kasa Christina Segal-Knowles, Amirka za ta so a kammala yarjejeniyar ta TTIP kafin karshen wannan shekara:

Argentinien Container im Hafen von Buenos Aires
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Perez Moreno

"Na samu bayani daga wakilan tawagarmu da ke tattaunawar cewa komai na tafiya daidai. Shugaban kasa ya ba su izinin kawo karshen tattaunawa a wannan shekara. Kuma a kan haka suke aiki, za a kuma kammala kafin karshen wa'adin wannan gwamnati wato karshen shekara."

A tsakanin kasashen EU ana fargabar cewa yarjejeniyar cinikin da ake shirin kullawa za ta raunata dokokin yaki da gurbata muhalli da na kyautata zamantakewa. Ana ta kuma gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yarjejeniyar ta TTIP. Hatta a Amirka ma ana samun masu sukar lamirin yarjejeniyar ciki har da Hillary Clinton 'yar takarar neman shugabancin Amirka karkashinn jam'iyyar Democrat da Donald Trump na jam'iyyar Republicans.