1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya karu tsakanin masarautar Kano da gwamnati

Nasir Salisu Zango
June 15, 2019

A jihar Kano da ke Najeriya rikicin gwamnati da fadar masarautar Kano ya kara dagulewa bayan wata babbar kotun jiha ta ki amincewa da bukatar masu nada sarkin Kano na hana sabbin sarakunan da aka kirkira ci gaba da aiki.

https://p.dw.com/p/3KUSs
Sanusi Lamido Sanusi Gouverneur Zentralbank Nigeria
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/Getty Images

Babbar kotun jihar Kano da ke zama karkashin jagorancin Justice A T Badamasi ce ta yi kwarya-kwaryar hukunci wanda ya hana bukatar masu nada sarkin Kano da ke kalubalantar nadin sabbin sarakuna 4 da aka yi a Kano, sai dai masana a fannin shari'a sun ce wannan hukunci ba yana nuna kawo karshen shari'ar ba illa dai wata bukata ce da aka nema a aiwatar kafin kammala shari'a wacce kuma alkalin yaki amincewa da ita har sai an kammala shari'ar, lamarin da ke nufin cewar har yanzu dai shari'a tana nan kuma akwai sauran rina a kaba a cewar Barrista Abba Hikima lauya mai zaman kansa a Kano.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano da ke NajeriyaHoto: Salihi Tanko Yakasai

Ba ya ga wannan shari'ar batun sulhu tsakanin gwamna da Sarkin Kano shi ma dai ya kara dagulewa biyo bayan amsar wasikar da kwmaishinan yada labarai na jihar Kano Comrade Muhammad Garba ya rubuta yana mai shimfida wasu sharudda da ya ce sai an bisu sannan sulhu zai tabbata tsakanin gwamna da sarki cikin sharuddan har da batun cewar lallai sai Sarki Muhammadu sunusi na 2 ya bai wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje hakuri.

Wannan batu dai ya kara mayar da hannun agogo baya dangane da samo bakin warware rigimar da ta ki ci ta ki cinyewa tsakanin gwamnati da masarautar Kano har ta kai wannan batu na neman zama wata babbar barazana ga tsaro a jihar Kano.