1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin Najeriya da Kenya

June 21, 2013

Hukumomin Najeriya sun kama jirgin Kenya a birnin Lagos, sakamakon takaddamar da ta shiga tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/18uFL
Hoto: AP

Tun bayan cafke Jirgin kasar Kenya a birnin Lagos na Tarayyar Najeriya, har yanzu jami'an da ke cikin jirgin na cikin kasar ta Nigeria tare da 'yan Nigeria uku da ake zargi da fataucin Kwayoyi, na hannun ofishin jakadacin kasar Kenya a yayin da 'yan Nigeria ke hannun hukumomin kasar.

Jirgin dai ya shiga Nigeria ne tun a ranar uku ga Juni inda hukumomin kasar ta Nigeria suka cafke shi bisa zargin ya shigo kasar ne ba tare da bin ka'idoji ba kamar yarda doka ta tanada .

DW_Nigeria_Integration2
Hoto: Katrin Gänsler

To sai dai Rahotanni daga can Kasar ta Kenya, na cewa Shugaban kasar sabo da aka zaba Uhuru Kenyatta, na yin bita da kulli ga 'yan Nigeria bisa kin goyan bayansa a zaben da ya gabata. Masu iya magana dai kan ce ruwa ba ya tsami banza.

Bincike dai da baya karya ya tabbatar da cewa 'yan Nigeria da ake zargi da fataucin muggan kayan maye ba su a cikin jerin sunayen da ake zargi da yin hakan a cikin kasar ta Nigeria koda a cikin gida ko ketare .

Babban Janar Manaja na hulda da jamma'a na hukumar sufurin jiragen sama ta Nigeria Mr Yakubu Dati ya ce an dai cafke mutane 18 cikin su 'yan Nigeria uku ne, a yayin da 'yan Kasar Kenya su 15. Kuma ana ci gaba da bincike na sanin gaskiyar lamari kuma da zarar an kammala zaa iya sallamar yan kasar ta Kenya matukar basu da sauraN bayani ga hukumar Nigeria .

Baya ga batu na zaman doya da manja a tsakanin kasashen biyu sai kuma yarfe irin na siyasa inda kan haka ne na tuntubu mai ba da shawara ta fannin siyasa ga Shugaban kasar Najeriya Alhaji Ahmed Gulak kan anya babu batu na siyasa da take kadawa a tsakanin kasashen biyu nan take ya ce batu na cafke jirgin da ya shigo Najeriya ba tare da bin doka ba, babu batu na siyasa to ko wace siga. Yana mai cewa duk kasar da ta ki bin dokar Najeriya idan ta shigo za a dauki mataki a kanta saboda haka ba batun siyasa a tsakanin kasashen biyu .

Uhuru Kenyatta Präsident von Kenia
Hoto: Reuters

Malam Mohammad Abdullahi mai sharhi ne kan alamurran kasa ya ce Najeriya dai kasa ce uwa ga sauran kasashen Afrika baki daya in da kamata ya yi a hau kan kujerar sulhu domin samun mafita .

Da zaarar an kammala bincike za a sallami 'yan kasar ta Kenya tare da tawagar baki daya.

Mawallafi: Masur Bala Bello
Edita: Zainab Mohammed Abubakar