1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Taliban ta haramta a saurari DW a Afghanistan

March 28, 2022

DW ta ce matakin zai tauye wa Afghanistan ci gaban da fadin albarkacin baki ke kawo wa kasa. Shugaban DW ya ce za su yi duk abin da za su iya wurin ganin sun isar da rahotannin tashar ga mutanen Afghanistan.

https://p.dw.com/p/498RR
Media use in 2030 - Will individualization end mass communication? | DW Global Media Forum 2021
Hoto: Philipp Böll/DW

Hukumar gudanarwa ta tashar DW ta tabbatar da cewa 'yan kungiyar Taliban masu mulki a Afghanistan sun sanya tashar cikin jerin kafofin yada labaran ketare irinsu BBC da VOA da ta haramta sanya shirye-shiryensu a fadin kasar. 

A cikin sanarwar da babban daraktan tashar DW Peter Limbourg ya fitar a wannan Litinin, ya nuna damuwa kan matakin na Taliban. 

Sai dai mataimakin mai magana da yawun Taliban  Inamullah Samangani ya ce sun hana yada shirye-shiryen DW da BBC da VOA a sakamon yadda ma'aikatan wadannan kafofin yada labarai ke sanya tufafin da suka saba wa ka'idar Taliban. Ya kuma ce lokaci zuwa lokaci kafofin yada labaran na yada rahotannin da suka ci karo da addini da al'adar mutanen Afghanistan.