1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin Asiya ya yi kaɗan a yaƙi da Ebola

Yusuf BalaNovember 4, 2014

Da dama cikin ƙasashen a yankin Asiya na nuna halin ko in kula a ƙoƙarin da duniya ke yi na ganin an kawo ƙarshen cutar Ebola a yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1DgPc
Jim Yong Kim Präsident Welt Bank
Jim Yong Kim shugaban Bankin DuniyaHoto: picture-alliance/AP Photo/Seth Wenig

Duk kuwa da ƙwarewar da wadannan ƙasashe ke da ita a fannin ma'aikatan kula da lafiya a cewar shugaban bankin duniya Jim Yong Kim a ranar Talatan nan ba sa abin da ya dace.Mista Kim ya faɗi a taron manema labarai a birnin Seoul cewar ƙasashe da dama a yankin na Asiya da za su iya ba da gudunmawa ba sa yi musamman idan ana maganar tura jami'an lafiya .

Dubban ma'aikatan lafiya a ke buƙata a yaki da wannan annoba, tun lokacin ta kafa tarihi a shekarar 1976, ya zuwa yanzu ta kashe sama da mutane 5000 a ƙasashen yammacin Afirka, mafi akasari a Guinea da Saliyo da Laberiya.