1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai ta cimma matsaya bisa batun muhalli

Salissou BoukariSeptember 18, 2015

Kasashen membobi a kungiyar Tarayyar Turai sun amince a wannan Jumma'a kan wasu manufofin na bai daya, da za su gabatar a babban taro kan muhalli da zai gudana a birnin Paris na Faransa.

https://p.dw.com/p/1GYvL
Hoto: picture alliance / dpa

Kasashen dai sun amince da rage gurbataccan hayaki mai bata muhalli da kashi 40 cikin 100 ya zuwa shekara ta 2030. Ministocin Muhalli 28 na kungiyar da suka yi wani zaman taronsu a birnin Brussels, sun kuma dauki wani dogon buri na rage kashi 50 cikin 100 ya zuwa shekata ta 2050. A halin yanzu dai ana iya cewa kungiyar ta Tarayyar Turai ta samu wata madogara da zata dukufa a kanta a babban zaman taron muhawara kan muhalli da zai gudana daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 11 ga watan Disamba masu zuwa. Da ma dai kafin babban zaman taron na birnin Paris, an bukaci ko wace kasa ta wallafa irin gudun mowar da zata bayar a fannin yaki da gurbacewar muhallin.