1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin sabuwar shugabar rikon kwaryar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

January 23, 2014

Catherine Samba-Panza ta yi nasarar shiga cikin jerin mata da ke rike da mukamin shugabannin kasashe a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/1Aw7b
Zentralafrikanische Republik Interimspräsidentin Catherine Samba-Panza 23.01.2014
Hoto: Reuters

Zaben da 'yan majalisar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka yi wa Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar kasar na wucin gadi. Hakan ya janyo ta zama mace ta uku ke nan, da ke rike da madafun iko cikin kasashen Afirka bayan na kasashen Laberiya da Malawi.

Catherine Samba-Panza ta samu lashe zaben yayin zagaye na biyu, abin da ya bata damar zama mace ta farko da ta jagoranci kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tun bayan samun 'yancinta daga Turawan mulkin mallaka na Faransa a shekarar 1960. Ta fara da neman hadin kai:

"Daga wannan rana na zama shugabar daukacin al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya baki daya, babu wani bambanci."

'Yan takara takwas ne suka fafata wajen neman kujerar shugabancin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da suka hada da mata biyu, da 'ya'yan tsoffin shugabanni biyu. Yanzu tana da jan aikin sake hade kan kasar bayan murabus da Shugaban wucin gadi Michel Djotodia ya yi cikin wannan wata na Janairu. Kuma kungiyar 'yan tawayensa ta Seleka ce ta kwace madafun iko, abin da ya jefa kasar cikin rudani na siyasa.

Zentralafrikanische Republik Michel Djotodia Verhandlungen Ndjamena Tschad
Taron shugabannin yankin tsakiyar AfirkaHoto: Brahim Adji/AFP/Getty Images

Dalilan nadin Catherine Samba-Panza

Djotodia ya zama Musulmi na farko da ya mulki kasar, bayan kifar da gwamnatin Francois Bozize a watan Maris na shekarar da ta gabata.

Sabuwar shugabar ta zama magajiyar garin birnin Bangui cikin watan Maris, lokacin da kungiyar Seleka ta kwace madafun iko, amma bata da alaka mai karfi da Michel Djotodia. Kuma babu dangantakar da take da shi da 'yan Seleka.

Catherine Samba-Panza 'yar shekaru 59 da haihuwa, an haife ta a kasar Chadi da ke makwabtaka da Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya, ta kasance masaniyar harkokin shari'a wadda ta yi karatu a Faransa, sannan tana da aure da 'ya'ya uku. Kafin shiga harkokin siyasa, ita masaniya ce ga dokokin kasuwanci, tana kuma cikin kungiyoyin mata.

Zentralafrikanische Republik Catherine Samba-Panza & Laurent Fabius 23.01.2014
Catherine Samba-Panza da ministan wajen Faransa, Laurent FabiusHoto: Reuters

Kyakkyawan fata ga Catherine Samba-Panza

Akwai fata kan sabuwar Shugabar za ta taimaka wajen magance matsalolin, kamar yadda Paul Simon Handy na wata cibiyar kula da lamuran tsaro da ke kasar Afirka ta Kudu ke cewa:

"Wannan wata ce wadda ta dace, wadda za ta hadawa maimakon ta raba kai."

Bayan fitowa daga zauren zaben, Desire Nganga Kolingba, wanda ya zo na biyu yayin zaben, ya fara da taya sabuwar shugabar murna:

"Ina taya Samba-Panba murnar lashe zabe, ina neman sauran 'yan uwa mu hada kai, mu taimakawa Samba-Panza, domin aikin da zai kawo wa kasa bunkasa."

Wani babban kalubalen da ke gaban Shugabar kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Catherine Samba-Panza shi ne kwance damarar kungiyoyi masu dauke da makamai. Tuni ta yi kira gare su:

"Ina kira ga 'ya'yana Anti-Balaka kan ku ajiye makamai a matsayin martani bisa wannan zaben da aka yi mun. Haka kuma 'ya'yana Saleka na kungiyar 'yan tawaye ku ajiye makamai."

Kasar tana gab da rushewa lokacin da aka zabi Catherine Samba-Panza a matsayin shugaba, kuma yanzu tana da jan aikin wajen tabbatar da zaman lafiya da shirya zabe zuwa watan Fabrairu na shekara mai zuwa ta 2015.

Mawallafi : Fischer, Hilke/ Suleiman Babayo
Edita : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani