1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Tedros Adhanom Ghebreyesus shugaban WHO

Usman Shehu Usman
July 6, 2017

https://p.dw.com/p/2g3SD

To  Shi dai Tedros Adhanom Ghebreyesus, dan kasar Habasha ne kuma an haife shi ne a ranar 03.03.1965 a birnin Asmara, na kasar Erythreya. An zabe shi a matsayin sabon babban daraktan hukumar lafiya ta duniya, WHO ko kuma OMS, wanda ya zamo dan Afirka na farko da zai rike wannan babbar ma'aikata ta Majalisar Dinkin Duniya. Kuma abun da zai sa a gaba a jagorancin hukumar a cewarsa, shi ne na yin komai cikin haske.

Tedros, mutum ne da ya yi fice a fagen siyasa da bangaren ilimi da kuma zama babban jami’in kula da lafiya. Ya fara aiki ne a ma’aikatar lafiya ta kasarsa a shekara ta 1986 jim kadan da kamala karatunsa na jami’ar birnin Asmara. Ya rike mukamin ministan lafiya a kasarsa ta Ethiopia wato Habasha tsakanin shekarun 2005 zuwa 2012 da kuma ministan harkokin wajen kasar daga shekara ta 2012 zuwa 2016. 

A matsayinsa na sanannen mai bincike kan cutar nan ta zazzabin cizon sauro wato Malaria. Tedros ya sami yabo da dama saboda kirkira tare da bullo da dabarun magance matsalolin lafiya masu yawa da ya yi. Daga ciki akwai batun daukar mata dubu 40 da suka kasance jami’an kula da lafiya  da suka taimaka wajen rage mace-macen kananan yara a shekara ta 2011. Haka ma ya yi rawar gani a fannin daukar kwararrun likitoci da ungozomai. 

Tedros Adhanom Ghebreyesus ehem. Außenminister Äthiopien
Hoto: DW/T. Woldeyes

An zabe shi a matsayin jagoran shirin yaki da cutar HIV  da tarin fuka da kuma na zazzabin Malaria a shekrarar 2009, matsayin da ya rike tsawon shekaru biyu. A watan Janairun bara wato 2016, taron kungiyar Tarayyar Afirka ta AU,  ya amince takararsa ta neman matsayin hukumar lafiya ta duniyar daga Afirka,  ya kuma yi nasara an zabe shi  a ranar 23 ga watan Mayun bana. Kuma a yanzu shi ne wanda nauyin  jagorancin matakan dauka kan duk wani kalubale na kiwon lafiya,  da kuma shinfida tsarin kiwon lafiya na dukanninn kasashe membobi ya rataya a kanshi.

To Lokacin da aka zabe shi a wannan matsayi ya yi wani jawabi a can cibiyar hukumar da ke birnin Jiniva, ko mi ya ce?
Ya ce: " Ba zan taba mantawa da mutanen da muke yi wa aiki ba, domin abubuwan da muke yi, muna yin su ne domin wadanda muke yin ayyukan dominsu. Domin ba su nan birnin jiniva inda muke wannan jawabi, amma suna can suna fama da cutuka iri-iri wadanda ake iya kauce wa kamuwa da su, ko kuma ragewa harkokin binciken kiwon lafiya karfi. Ga baki daya zamu kawo ci gaba a fannin kiwon lafiya 'yan uwanmu maza da mata da ke da rauni sosai, wannan shi ne burin da na sa wa gaba."

A wannan Asabar din ce 01.07. 2017 Mista Ghebreyesus ya karbi ragamar jagorancin wannan babbar ma'aikata ta Majalisar Dinkin Duniya daga hannun 'yar kasar China Margaret Chan wadda ta jagoranci hukumar mai cibiya a birnin Jiniva na kasar  Suisland na tsawon shekaru shida hukumar da ke da ma'aikatan da yawan su ya kai dubu 8.000 da ke aiki a karkashita a fadin Duniya, wanda ya nunar da cewa hukumar ta WHO na daya daga cikin manyan ma'aikatu na Majalisar Dinkin Duniya, kuma zai kuma jagoranci hukumar ne na tsawon shekaru biyar.