Tsohon jami'in gwamnatin Saddam ya mutu
June 5, 2015Talla
Rahotanni sun bayyana cewa Tariq Aziz mai kimanin shekaru 79 a duniya ya mutu ne a asibitin al-Hussein da ke birnini Nasiriyah a wannan Jumma'a. Aziz wanda kotun kasar ta Iraqi ta yanke masa hukuncin kisa bisa rawar da ya taka a gwamnatin Saddam Hussein da ta janyo asarar rayukan dubun-dubatar al'ummar kasar iraqin, kafin rasuwarsa yana tsare ne a gidan yari da ke arewacin kasar inda ya ke jiran a aiwatar da hukuncin kisan da aka yanke masa. Tun a shekara ta 2010 ne dai aka yankewa Aziz hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai dai har ya rasu ba a aiwatar da hukuncin da aka yanke masan ba.