1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashe renon Ingila a Sri Lanka

November 16, 2013

Bayan da ƙasashe da dama suka ƙauracewa taron da ke gudana Colombo bisa zargin tafka manyan laifukan yaƙi, David Cameron na Birtaniya ya buƙaci da a gudanar da bincike kan wannan lamari

https://p.dw.com/p/1AIuN
British Prime Minister David Cameron arrives at 10 Downing Street in central London on August 27, 2013, after returning early from a holiday to address the Syria crisis. Cameron will decide later on August 27 whether to recall parliament from its summer recess to debate a possible military intervention in the wake of a chemical weapons attack that Washington, London and Paris believe was carried out by the Syrian regime, Downing Street said. Cameron is expected to chair a meeting of the National Security Council to discuss Syria on August 28. AFP PHOTO / CARL COURT (Photo credit should read CARL COURT/AFP/Getty Images)
David Cameron Firaministan BirtaniyaHoto: Getty Images/Afp/Carl Court

Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin an gudanar da bincike mai zaman kan shi kan zarge-zargen aikata manyan laifukan yaƙi a ƙarshen yaƙin basasar ƙasar Sri Lanka, wanda ya ɗauki tsawon shekaru 26, abin da kuma ya fusata shugaban ƙasar Sirilankar Mahinda Rajapaksa, inda aka rawaito shi yana cewa duk mai ruwa kada ya zagi kada, bayan da Mr Cameron ya ce ya kamata ƙasar ita ma ta gudanar da nata binciken kafin watan Maris na shekara ta 2014 ko kuma ta fiskanci tuhuma daga kwamitin ƙasa da ƙasa.

Firaministan Birtaniyan David Cameron ne ya gota kowa wajen yin suka ga yanayin da ake tafiyar da harkokin kare hakkin bil adaman ƙasar, a taron Commonwealth ko kuma ƙasashe renon Ingilan dake gudana a Colombo babban birnin ƙasar.

Dakarun Sri Lankan dai sun murƙushe 'yan awaren Tamil Tigers a dagan ƙarshe na yaƙin da aka yi a shekara ta 2009 a wata maƙarƙashiyar da ake zargin ɗan uwan shugaba Rajapaksa, wato Gotabaya Rajapaksa da ƙullawa lokacin yana riƙe da muƙamin ministan tsaro.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh