1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen ’yan ba ruwanmu ya yi kira ga Isra’ila da ta janye dakarunta daga zirin Gaza.

September 14, 2006
https://p.dw.com/p/BujZ

Mahalarta taron ƙoli, na ƙasashen ’yan ba ruwanmu da ake yi a birnin Havana na ƙasar Cuba, sun yi ikira ga Isra’ila da ta janye dakarunta daga zirin Gaza, ta sako duk fursunonin Falasɗinawan da take tsare da su, sa’annan kuma ta biya Falasɗinawan diyya saboda ɓarnar da sojinta suka yi musu.

Wani kundin ƙudurin da shugabannin ƙasashen za su rattaba hannu a kai, ya nuna damuwa ga taɓarɓarewar al’amura a yankunan Falasɗinawan da Isra’ilan ta mamaye, a cikinsu kuwa har da birnin Ƙudus. Ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar sun yarje kan wani kundin kuma, wanda ke Allah wadai da Isra’ila saboda ci gaba da halaka Falasɗinawa da ji musu raunuka da rukunan sojinta ke ta yi ba gaira ba dalili. Kazalika kuma, sanarwar da ministoocin suka bayar, ta yi kakkausar suka ga wasu ƙasashen da suka soke tallafin da suke bai wa Hukumar Falasɗinawan, tun da ƙungiyar Hamas ta lashe zaɓen da aka gudanar a cikin watan Janairu. Amirka dai na kan gaba wajen ɗaukar ƙungiyar Hamas ɗin tamkar ƙungiyar ’yan ta’adda.