1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Amirka na taro da shugabannin Afirka

December 14, 2022

An fara taron koli tsakanin gwamnatin Amirika da wasu shugabannin kasashen nahiyar Afrika 49, lokaci da gwamnatin Shugaba Joe Biden take neman hanyoyin da za ta rage karfin tasirin kasashen Chaina da Rasha a Afirka.

https://p.dw.com/p/4KuJq
Amirka I Birnin Washington | Taron Amirka da Afirka
Taron Amirka da AfirkaHoto: Evelyn Hockstein/AP/picture alliance

A wannan taro na kwana uku dake mayar da hankali kan batutuwa dabam-dabam da suka hada da; kasuwanci, tsaro, ciniki, kare hakkin dan Adam, yanayi, kungiyoyi masu zaman kansu, da tasirin da ‘yan asalin nahiyar Afrrka suke takawa a nan Amirka, domin nuna da gaske take yi, gwamnatin Shugaba Joe Biden ta Amirka ta bakin mai bada shawara kan harkokin tsaron kasa Jake Sullivan, ta baiyana aniyar kashe dala bilyan 55 a fannin harkokin tsaro dana tattalin arziki a nahiyar Afirka cikin shekaru uku nan gaba.

A wannan Laraba ake kyautata zaton mai masaukin baki Shugaba Biden zai yi jawabi a zauren tattauna al'amuran tattalin arzikin duniya, musanman wadanda suka shafi alakar kasarsa da Afirka, majiyoyi sun yi tsokacin cewa, ana sa ran shugaban na Amurika, zai yi amfani da damar wajen nuna goyon baya na ba iwa nahiyar Afirka kujerar wakilin dindindin a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

Amirka | Taron Amirka da Afirka | Antony Blinken da Felix Tshisekedi
Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken da Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukaradiyyar KwangoHoto: Evelyn Hockstein/Pool via AP/picture alliance

Bisa la'akari da yadda kasuwanci a tsakanin nahiyar Afirka da kasar Chaina ya kai dala bilyan 254 a shekara, da kuma yadda Rasha take yin kutse a nahiyar, musanman ta fuskar cinikin makamai, ba abin mamaki ba ne, idan gwamnatin Biden ta yunkura wajen rage kaifin wadannan kishiyoyi biyu a Afirka. Sai dai ayar tambaya a nan ita ce, ko a wannan karon Amirka za ta nuna da gaske take yi, duba da makamancin wannan taron koli da tsohuwar gwamnatin tsohon Shugaba Barack Obama ta taba shiryawa a cikin shekarar 2014.

Duk da yadda gwamnatin Shugaba Biden take kokarin kyautata alaka da Afrika, ga alama har yanzu ba ta huce ba, game da halayyar wasu shugabannin kasashen Afirka. Domin kuwa ba ta gaiyaci kasashen da kungiyar hadin kan Afrika ta AU ta dakatar ba, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a cikin kasashen; watau kasashen Mali, Sudan, Guinea da Burkina Faso. A cikin shekara mai zuwa, ake kyautata zaton Shugaban na Amirka Joe Biden zai jagoranci wata babbar tawagar kasarsa domin kai ziyara wasu kasashen nahiyar Afrika.