1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Commonwealth cikin rarrabuwar kawuna

November 15, 2013

Shugabannin ƙasashe da dama sun yi gargaɗin cewar ba zasu halarci taron ba, wanda ake gudanarwa a birnin Colombo a kan zargin cin zarafin bil adama da ake yi wa shugabannin ƙasar.

https://p.dw.com/p/1AI6u
***Unabhängigkeitsfeier mitten im Bürgerkrieg - Sri Lanka hat 60 Jahre nach der britischen Kolonialherrschaft nicht viel zu feiern, Heinzle*** Sri Lanka's President Mahinda Rajapaksa addresses the nation during an event to celebrate Sri Lanka's 60th Independence Day in Colombo, Sri Lanka, Monday, Feb. 4, 2008. Sri Lanka celebrated its 60th independence anniversary Monday with parades, speeches and an intense security clampdown aimed at halting a growing wave of attacks blamed on separatist rebels that have killed scores of civilians across the country. (AP Photo/Gemunu Amarasinghe)***Zu Heinzle, Sri Lanka wieder im Bürgerkrieg - Nach Ende des Waffenstillstands***
Hoto: AP

Nan gaba kaɗan ake shirin buɗe taron ƙasashe rainon Ingila wato Commonwealth a birnin Colombo na ƙasar Siri Lanka. Taron wanda ke cike da cece-ku -ce dangane da zargin da ake yiwa hukumomin ƙasar da aikata ta'addi da kuma cin zarafin bil adama, a lokacin yaƙin da gwamnatin ta yi da 'yan tawayen Tamouls.

Shugabannin da dama na ƙasashen duniyar manba a cikin ƙungiyar sun ce ba zasu halarci taron ba, a cikin har da fira minista Kanada Stephen Harper da kuma takwaransa na Indiya Manmohan Singh. Tuni dai da aka ba da rahoton cewar firaminstan Ingila David Cameron ya isa a birni Colombo. A ƙarshen yaƙin da gwamnatin ta Siri Lanka ta kawo da 'yan ƙungiyar ta Tamouls wanda ta murkushesu a shekarun 2009. MDD ta ce mutane kusan dubu ɗari suka mutu. To sai dai hukumomin na Siri Lannka na musaunta zargin cewar sun yi ba daidai ba a lokacin yaƙin.

Mawallafi : Abdourhamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu