1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tattalin arziki na Davos bunkasa fusahar zamani

Becker, Andreas SB
January 23, 2019

Juyin-juya hali na na'urorin zamani na cikin abin da taron tattalin arziki na duniya da ke gudana a birnin Davos na Switzerland ya mayar da hankali. Shin muna bukatar sabbin na'urrorin da za a rika sauyawa?

https://p.dw.com/p/3C23q
Weltwirtschaftsforum in Davos
Hoto: picture-alliance/dpa/Keystone/G. Ehrenzeller

Taron na wannan shekara yana da taken juyin-juya na hudu na na'urori, yayin da masu ruwa da tsaki kan ci-gaba a duniya suka hadu aa canza ra'ayoyi da aka saba. Satya Nadella ke jaraoncin kamfanin na'urar kwamfuta ta Microsoft daya daga cikin manyan kamfanonin duniya na zamani: "Muna lokaci mai tsauri na tarihi, inda ci-gaban zamani ke kara shi ko wane sako a bangaren tattalin arziki. Saboda haka gasa na juna na zama wani bangaren rayuwa al'umma duniya a wani tunanin tana zama na'ura kwamfuta."

Weltwirtschaftsforum in Davos
Hoto: picture-alliance/dpa/Keystone/G. Ehrenzeller

Ci-gaban zamani na kara sauya yadda lamura ke tafiya inda kananan ayyuka ke kara bacewa. Misali ana kara neman hanyar tafiyar da shaguna ba tare da musu karbar kudi ba, da motoci masu tuka kansu, mai zai faru da milyoyin mutane idan ayyukan sun bace. Wannan na zama kalubale a kasashe masu karfin tattalin arziki.

Yayin da a kasashe masu tasowa ake fama da tarin matsaloli gami da milyoyin 'yan gudun hijira wadanda suke tsere daga gidajensu sakamakaon tashe-tashen hankula. Abu mai kamar wuya a yi tafiyar ta zamani tare da su. Mohammed Hassan dan shekaru 24 da haihuwa ya shafe kimanin shekaru 20 yana rayuwa a sasansanin 'yan gudun hijira na Kakuma da ke arewa maso gabashin Kenya, inda aka zabeshi a matsayin shugaban sansanin da kimanin mutane 185,000. Ya kasance cikin mahalarta taron na tattalin arziki na duniya a birnin Davos, wanda kuma ya ce ci gaban wani babban kalubale a game da batun 'yan gudun hijira.