1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin EU kan batun ficewar Birtaniya

Gazali Abdou TasawaJune 28, 2016

A yau ne a birnin Brussels ake bude taron koli na shugabannin kasashen Turai wanda ke a matsayin na farko tun bayan matakin 'yan Birtaniya na kada kuri'ar amincewa da ficewar kasarsu daga Kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/1JEkn
Deutschland Berlin PK Merkel Renzi und Hollande
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Taron na da burin matsa kaimi ga kasar Birtaniyar na ta gaggauta aiwatar da matakin ficewa daga Kungiyar ta EU domin kaucewa hadarin koma bayan harakokin kasuwancin kasashen Kungiyar, kana yana da burin daukar matakan rigakafin hanawa wasu kasashen Turan bin sahun kasar ta Birtaniya.

A wani taron share fagen wannan taron koli da suka yi a jiya a birnin Berlin, shugabannin kasashen Jamus da Faransa da kuma Italiya sun jaddada matsayinsu na yanke kauna ga duk wata tattaunawa da Birtaniyar idan har ba ta gabatar da takardar neman ficewar tata ba daga Kungiyar ta EU a hakuamance.

Shugabannin kasashen uku na kuma shirin gabatar wa da taron kolin na EU da wani sabon shirin da zai shafi harakokin da suka hada da batun inganta tsaro da na samar da aIyyukan yi a tsakanin kasashen Kungiyar.