1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20 na fuskantar kalubale daga Trump

November 29, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump na nuna halin ko in kula kan yin aiki tare da kasashen G20 dangane da batun tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/39AX3
Argentinien Buenos Aires G20 Gipfel
Taron G20 a AjantinaHoto: picture-alliance/dpa/R. Hirschberger

Ga mutane irinsu shugaban kasar Amirka Trump ba su da wata sha'awar yin aiki tare da kasa da kasa. To sai dai ra'ayoyin sauran shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 masu karfin tattalin arziki a duniya, sun bambanta da na Trump. Kungiyar kasashen G20 din dai za su gudanar da taronsu karo na 10 daga ranar Jumma'a 30 ga wannan wata na Muwamba zuwa Asabar daya ga watan Disamba mai zuwa. Taron dai na zaman na farko da ke gudana a yankin Latin Amirka. Shugaban kasar Ajentina wanda ke zama mai masaukin baki, na fuskantar matsalar tabarbarewar tattalin arziki a kasarsa, a dangane da haka taron kasashen 20 masu karfin tattalin arziki, shi ne babban abin da shugaban zai iya nunawa makwabtansa irin kokarin da yake yi domin zawarcin masu zuba jari.

Kalubalen masassarar tattalin arziki.

To sai dai ba kasar Ajantina ce kadai ke fuskantar matsalar tattalin arzikin ba, don haka taron na bana ya zo ne a lokacin da ake bukatar kasashen duniya su hada kai domin ceto kasashen da yanzu suke dab da fadawa cikin rikicin tattalin arziki. Christine Lagarde shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, ta yi karin haske kan matsalolin da duniyar ke fuskanta.

Indonesien Jahrestagung von IWF und Weltbank Christine Lagarde
Shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya Christine LagardeHoto: picture-alliance/AP Photo/F. Lisnawati

"Tabbas abun ya nuna irin tasirin koma bayan tattalin arziki da ake fama da shi. Wani abu mai muni shi ne, tattalin arzikin duniya baki daya zai samu koma baya da kusan digo biyar. Wannan shi ne hasashenmu wanda za mu iya bayyana wa kowa."

Babban abin da ake bukatar shugabannin kasashen na G20 su yi nazari a kai dai shi ne halin da manyan kamfanoni da ke gudanar da ayyukansu tsakanin kasa da kasa ke ciki, Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya nunar da cewa akwai bukatar yin aiki tare. Sai dai irin wannan aiki tare da shugaban kasar Afirka ta Kudu ke fatan samu daga huldarsu da kasashen da suka ci-gaba, yana fuskantar hatsari, idan aka yi misali da manufofin shugaban kasar Amirka Donald Trump. Ana dai sa ran ko taron na kungiyar G20 a kasar Ajantina ka iya yayyafa ruwa kan irin wadannan matsalolin kasuwanci tsakanin kasa da kasa, kasancewar kasashen mambobbin kungiyar ta G20 ne ke rike da kaso 80 cikin 100 na karfin tattalin arzikin duniya.