1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harakokin tsaro na ƙasashen EU.

March 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5b
V

Ministocin harakokin tsaro na ƙasashe membobin ƙungiyar gamayya turai, sun yi zamman taro yau, a birnin Innsbruck, na ƙasar Austriya.

Mahimman batutuwan da ke ajendar wannan taro, sun haɗa da aika dakarun shiga tsakani a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo, da batun girka assusun talafawa bincike, a kan harakokin tsaro a nahiyar turai.

Kazalika mahalarta taron, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da al´amuran ta´adanci a dunia.

A ƙarshen watan desember da ya wuce, Majalisar Ɗinkin Dunia, ta buƙaci ƙungiyar gamayya turai, ta aika dakarun shiga tsakani, a Jamhuriya Demokraɗiya Kongo da ke fama da rikicin tawaye.

A tsarin da su ka shirya, ƙasashen EU za su tura bataliya guda da za ta ƙunshi sdakaru dabu 1 zuwa 1250, a wannan yanki na tsakiyar Afrika.

Saidai ,a sakamakon mahaurorin da su ka gudanar yau, a a kan wannan batu, ministocin tsaron EU, ba su cimma matsaya ba, ta bai ɗaya, a game da aika wannan runduna, amma za su ci gaba da tuntubar juna, kamar yadda ministan harakokin tsaron Jamus, Franz Josef Jung ya bayyana.