1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

taron ministocin wajen G8

June 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6K

Ana kyautata zaton taron kungiyar nan na kasashe 8 masu cigaban masanaantu da zai guna a birnin Moscow,zai fitar da sanarwa dake kara matsin lamba wai ran ,ta mayar da martani kann shrin nuclearnta.Matsalolin sarrafa sinadran atom na Iran ,sune batutuwa da sakatariyasr harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice da ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da kuma Britania,zasu tattauna akai a taron sharan fage da ke gudana ayau.Bugu da kari anasaran ministocin zasu tabo rigingimun yankin gabas ta tsakiya musamman na Izraela da yankin palasdinawa,wanda shine batu yanzu dayafi daukar hankalin duniya.