1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabannin Afirka a Amirka

Zainab MohammedAugust 3, 2014

Shugabannin nahiyar Afrika za su gudanar da taro tare da takwaransu na Amirka Barack Obama inda za su maida hankali kan kasuwanci da tsaro da taimakon raya kasa.

https://p.dw.com/p/1CoDF
Barack Obama Senegal Afrika-Reise Dakar
Hoto: Reuters

A gobe ne idan Allah ya kaimu kimanin shugabannin kasashen Afrika 50 za su halarci taro na kwanaki biyar a birnin Washington na Amirka, inda za su tallata wa Amurkan irin damarmaki na kasuwanci da ke da akwai a nahiyar da zummar ganin an samu masu zuba jari.

Yayin wannan taro dai ana sa ran Amirka za ta sanar da yarjejeniyar kasuwanci ta kimanin dala biliyan guda da za ta kulla da nahiyar baya ga kara daukar nauyin ayyukan kiyaye zaman lafiya da kuma kashe wasu makuddan kudade wajen samar da abinci a kasashen Afirka.

Tun da fari dai an zargi Amirka da yunkurin amfani da taron wajen maida martani ga China dangane da irin tasirin da Amirka ke da shi a Afrika, zargin da mahukuntan Amirkan suka yi watsi da shi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu