1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Tarayyar Turai

Suleiman BabayoJune 28, 2016

Tarayyar Turai tana taron farko bayan kuri'ar raba gardama da aka yi a Birtaniya na fita daga kungiyar kuma kasashen sun kawar da yuwuwar bayar da gata ga Birtaniya idan ta fice daga Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/1JF1J
Brüssel Brexit Gipfel David Cameron und Jean-Claude Juncker
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Firaminista David Cameron na Birtaniya da yake halartar taron kungiyar Tarayyar Turai karo na farko tun bayan da kasar ta kada kuri'ar raba gardama fice daga kungiyar, ya bukaci ganin sassan biyu sun ci gaba da aiki tare, da kuma duk lokacin da ake fara zaman raba gari an yi cikin mutunta juna.

Cameron ya shaida wa manema labarai a birnin Brussels na kasar Beljiyam da ke zama helkwatar kungiyar yana bukatar ganin hadin kai bisa cinikayya da tsaro.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kawar da yuwuwar kasar Birtaniya ta samu gatar da yanzu take da su bayan ficewa daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Yayin da take jawabi a majalisar dokokin kasar ta Bundestag karo na farko bayan Birtaniya ta kada kuri'ar fita daga cikin kungiyar Tarayyar Turai, Merkel ta ce sauran mambobin kasashen 27 suna karfin da ake bukata, kuma za su tattaunawa da Birtaniya amma sai bayan kasar ta kaddamar da aikin da kashi 50 na yarjejeniyar Lisbon da ta tanadi hanyoyin kasa za ta fita daga Tarayyar Turai.