1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na fuskantar barazanar 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afarJanuary 20, 2016

Batun kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai da ta'addanci da faduwar farashin man fetur da kuma batun sauyin yanayi na neman mamamye taron tattalin arzki na duniya a birnin Davos.

https://p.dw.com/p/1HhEA
Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck
Shugaban kasar Jamus Joachim GauckHoto: Reuters/R. Sprich

Taron wanda ake gudanarwa a yanzu haka a kan tattalin arzikin duniya na gudana ne a birnin Davos na kasar Switzerland. A jawabinsa Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck ya bayyana matsalar 'yan gudun hijira a matsayin wata jarrabawa da nahiyar Turai ke fuskanta ya na mai cewa:

"Bincike na baya bayan nan da taron tattalin arziki na duniya ya gudanar, na nuni da cewa babban kalubalen da duniya za ta fuskanta a gaba shi ne karuwar kwararar 'yan gudun hijira da ma barazanar da rayuwarsu ke fuskanta. Dubun-dubatar 'yan gudun hijira da ke neman mafaka a nahiyarmu, shi ne babbar jarrabawar da Tarayyar Turai ta taba fuskanta a tarihinta."

Daga cikin mutane 2,500 da ke halartar taron kan tattalin arziki na birnin na Davos dai akwai shugabannin kasashe 40, kana akwai kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki kan batun tattalin arzikin.