1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Turai da Afirka ya mamaye jaridu a Jamus

Mohammad Nasiru Awal
December 1, 2017

A wannan makon jaridun na Jamus gaba ki daya sun mayar da hankali a kan taron kolin shugabannin Tarayyar Turai da takwarorinsu na Afirka da ya gudana a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire.

https://p.dw.com/p/2odKB
Elfenbeinküste EU-Afrika-Gipfel in Abidjan
Hoto: Reuters/P. Wojazer

A labarin da ta buga dangane da taron jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce shugabanni fiye da 80 daga kasashen Kungiyar Tarayyar Turai EU da ta Tarayyar Afirka AU sun kwashe yini biyu suna tattaunawa game da damarmaki da kuma makomar matasan Afirka da akasari ba sa hangen wata makoma ta a zo a gani a nahiyar, dalilinsa ke sa su daukar kasadar yin tafiya mai hatsari zuwa Turai, tare kuma da duba hanyoyin dakile wannan kaura. Jaridar ta ce tun farkon taron kolin ya bayyana fili cewa ba za a iya rarrabe tsakanin batun matasan da kuma hijirar da suke yi don neman rayuwa mai kyau a wajen nahiyar Afirka ba. Saboda haka jaridar ta ce ya zama wajibi kasashen Turai da na Afirka su hada kai a matakan da za su dauka wajen sama wa matasan na Afirka da ke zama kashin bayan ci gaban kowace al'umma, damarmaki da za su iya ganin makomarsu a nahiyar ba sai sun yi kaura ba.

Oberschüler in Tahoua, Niger
Ilimi kalubalen matasan AfirkaHoto: DW

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel ta mayar da hankali kan matsalar tabarbarewar ilimi a kasashen yankin Sahel tana mai cewa ba bu wani yanki a duniya da ke da yawan wadanda ba su iya rubuta da karatu da ya kai yankin kasashe Afirka na kudu da Hamadar Sahara, to amma kasashen Turai ba sa zuba jari ko ba da tallafi na a zo a gani a wannan fanni.

Jaridar ta ce a kullum kasashen Turai sun fi mayar da hankali wajen neman hanyoyin magance musabbabin hijira a Afirka, kamar yadda batun ya zama jigo a taron kolin da aka yi tsakanin EU da AU a birnin Abidjan. To amma da wuya ake tabo batun ilimi, wanda a cewar jaridar inganta matsayin ilimi shi ne ginshikin samun wadata a nahiyar ta Afirka.

Libyen Flüchtlinge in der Nähe von Tripolis
Zama cikin rashin tabbasHoto: Getty Images/AFP/T. Jawashi

Jaridar ta ce ko da yake an dan samu ci gaba a Afirka musamman wajen rage yawan yara da ba sa zuwa makaranta, amma mafi yawan yara ba sa cin gajiyar matakan da ake dauka na inganta ilimi a Afirka.

Isra'ila za ta ba wa kasar Ruwanda dala dubu biyar kan kowane dan gudun hijirar da kasar za ta ba wa mafaka, inji jaridar Die Tageszeitung, inda ta ce bisa ga dukkan alamu Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda a wannan makon suka gana da Shugaba Paul Kagame na Ruwanda a birnin Nairobin kasar Kenya, yana son ya ga bayan bakin haure da ke a kasarsa. Alkalumma sun nuna cewa akwai bakin haure na Afirka su kimanin dubu 40 da ke zaune a Isra'ila. Jaridar ta ce idan Ruwanda ta amince da wannan tayi, da karfin tuwon za a kwashe 'yan Afirka daga Isra'ila zuwa kasar kuma duk wanda ya ki za a jefa shi kurkuku.