1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron wanzar da zaman lafiya a Ivory Coast

March 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6N

Shugabanni biyar na kasar Ivory Coast dake fada aji sun nuna amannar su ta yin aiki kafada da kafada da juna, wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar baki daya.

Shugabannin , wadanda suka fadi hakan a cikin takardar bayan taron da suka gudanar a jiya, sun tabbatar da cewa daga yanzu zasu dinga taruwa akai akai don ganin cewa ana aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a kai.

Wannan taron na masu fada aji a kasar dai, na a matsayin irin sa na farko ne da bai samu halartar mai shiga tsakani ba daga ketare.

Daga cikin mutanen da suka halarci wannan taro mai dimbin tarihi , akwai shugaba Lauret Gbagbo da shugaban yan tawaye Guillaume Soro da shugaban yan adawa na kasar, wato Alassane Quattara.

Ragowar sun hadar da tsohon shugaban kasar, wato Henri Konan Bedie da kuma Faraminista mai ci wato Charles Konan Banny.