1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin rikicin Masar ga 'yan gudun hijirar Afirka

September 4, 2013

'Yan gudun hijirar Afirka na fama da matsaloli daban daban a yunkurinsu na tsallaka wa zuwa Isra'ila domin samun aikin yi.

https://p.dw.com/p/19c0l
epa03261790 An inspector (R) from the Israel Immigration and Population Department check the documents of two African migrants, in a park in Tel Aviv, Israel, 12 June 2012. Israel is continuing with detaining and arresting African illegal migrants from South Sudan who they say are not political refugees but people who came to Israel seeking a better way of life, and they should be deported. Israeli media report that dozens of African migrants, most of them from South Sudan, have been arrested before dawn on June 11 in the southern resort town of Eilat, on the Red Sea. EPA/ABIR SULTAN +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A yayin da tashin hankali ke ci gaba da wanzuwa a Masar, 'yan gudun hijirar kasashen Afirka da ke neman tsallakawa Isra'ila bayan yada zango a kasar, na fuskantar cin zarafi daga masu safarar jama'a a mashigin Sina'i na kasar ta Masar.

Rikicin da ke ci gaba da wanzuwa a kasar Masar dai, ba ta tsaya ga 'yan kasar kadai ba, hatta baki - 'yan ci ranin dake neman zuwa Isra'ila wadda ke makwabtaka da Masar din, na fama da radadin rashin tsayayyiyar gwamnati a Masar.

Kahassay Woldesselasie, wanda ya bar kasarsa ta asali Eritriya da fatan samun rayuwa a kasar waje, kana ya fara da yada zango a kasar Sudan, ya ji labarin gurabun ayyuka masu romo a kasar Isra'ila. A kokarinsa na zuwa Isra'ilar ta hanyar Masar kuma ya fada hannun gungun masu safarar jama'a a Sina'i na Masar, kuma a cewarsa yayi nadamar halin da ya tsinci kansa a ciki:

"Su kan ce idan ba ka biya kuɗi ba za su kashe ka, saboda haka mutun ba shi da zaɓin da ya wuce kiran 'yan uwan shi a waya, sa'an ka shi ne su ansa wayar su biya kuɗin tun kafin a kai ga kashe ka"

An Israeli soldier stands atop an observation tower on the Israeli side of the border line with Egypt, near to the town of Taba, in the south of Egypt's Sinai Peninsula, Thursday, Oct. 27, 2011. An Exchange deal expected later Thursday between Egypt and Israel, to release US-Israeli national Ilan Grapel who was detained on suspicions of espionage since June 2011, for the release of 25 Egyptian prisoners held in Israel. (ddp images/AP Photo/Khalil Hamra)
Yankin da dakarun Isra'ila ke sintiri domin dakile shigo da bakiHoto: AP

'Yan Afirka da dama na cikawa a hannun masu safarar baki

Ko da shike Allah ya yi wa Woldesselasie gyadan dogo, domin kuwa 'yan uwansa dake kasashen waje sun tattara kudin da suka aikawa masu garkuwa da jama'a domin neman fansar suka sakeshi, amma akwai wadanda basu kai ga yin irin wannan nasarar ba. Hamdy al-Azazy, mai fafutukar kare hakkin jama'a da ke zama a garin al-Arish, hedikwatar arewacin Sina'i, ya ce ya sha haduwa da 'yan Eritriya da dama, wadanda ke shan azaba a hannun masu garkuwa dasu na tsawon makonni, a wasu sansanonin da suka samar a yankin. Ya ce a wasu lokuta ma, iyalansu na jin lokacin da bata-garin ke harbesu da bindiga - har lahira, ko kuma yanke wasu sassa na jikinsu. Abin bakin ciki kuma - a cewar al-Azazy, shi ne cewar, jami'an tsaron Masar na tsare wa tare da cin zarafin wadanda suka tsira bisa shiga kasar ba bisa ka'ida ba. Bugu da kari kuma ba sa hukunta masu tafka ta'asar:

Ya ce " Gungun masu safarar na samun tallafi daga sojoji da kuma shugaban rundunar 'yan sanda. Masu safarar mutane na biyan dimbin kudade domin kawo 'yan gudun hijira zuwa Sina'i."

Kididdigar da kungiyar kare hakkin jama'a ta Masar ta fitar dai, na nuni da cewar fiye da baki - 'yan Afirka 500 ne irin wannan matsalar ta rutsa dasu a shekarun baya bayannan, wadanda kuma suka gano gawarwakinsu yashe a hamadar sahara.

Israeli security forces secure the area after an attack, near the southern Israeli city of Beersheva, Monday, June 18, 2012. Unidentified militants crossed from Egypt's turbulent Sinai Peninsula into southern Israel on Monday, opening light arms and anti-tank fire on civilians building a security fence meant to fortify the porous border, defense officials said. One of the Israeli workers was killed, and two militants were gunned down by troops responding to the attack, the officials said. (Foto:Tsafrir Abayov/AP/dapd)
Dakarun Isra'ila a yankin Sina'iHoto: AP

Mafita game da azabtar da 'yan Afirka a Sina'i

A cewar, Gunter Meyer, na cibiyar nazarin harkokin da suka shafi kasashen Larabawa a jami'ar Mainz dake nan Jamus, wasu gungun bata-gari cikin mazauna yankin da a ka fi sani da suna Badawiyyin ne ke safarar:

"A tsibirin Sinai, za mu iya cewa yanayin tsaron na ci gaba da taɓarɓarewa. Wannan lamarin na da daɗaɗɗen tarihi, tun daga irin ƙyamar da ake nunawa al'ummomin Beduin na wani tsawon lokaci yanzu. Su Misrawan dai suna zargin, 'yan ƙabilar Beduin waɗanda ke zaune a yankin arewacin Sinai, da haɗa kai da kuma Israila da dillancin ƙwaya, kuma suna musu kallon jahilai"

Tun dai a shekara ta 1982 ne, Isra'ila ta janye daga yankin Sina'i, tare da mika ragamar kula da yankin ga hukumomin Masar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane