1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arziƙin Jamus ya zama abin alfahari

September 5, 2013

Jamus ce kaɗai ƙasar da ta ɗan tsira daga rikicin tattalin arziƙin Turai, kuma wannan nasara ce da manyan jami'yyu biyu a ƙasar ke dangantawa da rawar da suka taka.

https://p.dw.com/p/19cbp
#31056862 -made in germany © Goss Vitalij
Hoto: Fotolia/Goss Vitalij

Kashi ɗaya cikin huɗu na tattalin arziƙin Jamus na fitowa ne daga masana'antu, kuma masu kamfanonin na samun wakilci a Ƙungiyar Masana'antu na Jamus wadda ake kira BDI. Yawancin waɗannan masana'antu na gado ne mallakan iyalai daban-daban waɗanda ke ɗaukar ma'aikata aƙalla 500. Daga cikin ƙasashe masu arziƙin masana'antu babu ƙasar da ta kai Jamus nasara wajen raya kamfanoni cikin gida, wanda ke taimakawa wajen inganta ƙarfin tattalin arziƙint.

Babu shakka duk abubuwan da ake sarrafawa a cikin Jamus, mutane a duk faɗin duniya na saye musamman ma a ƙasashe masu tasowa, inda ake sayen abubuwa kamar motoci, manyan naurori da kuma magunguna. Kashi uku cikin huɗu na kayayyakin da ake sarrafawan na zuwa ne daga masana'antu masu ƙwarewar gaske. Kashi 90 cikin 100 na dukkan ayyukan bincike da raya ƙasa da ke gudana a Jamus ya rataya ne a wuyan masu masana'antu a yayinda sauran ƙasashen Turai suke da alhakin kimanin kashi 70 cikin 100, kenan Jamus na kan gaba a fanin masana'antu idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Turai. Ulrich Grillo shi ne shugaban Ƙungiyar masu masana'antun Jamus.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) spricht am 11.06.2013 auf dem Tag der Deutschen Industrie in Berlin. Im Laufe der Veranstaltung spricht auch noch der SPD-Kanzlerkandidat Steinbrück. Foto: Tim Brakemeier/dpa
Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa

Mahimmancin da Jamus ke baiwa masana'antu

"Jamus tana matsayin da ta ke a yau ne, saboda ta karkata ga inganta masana'antu ƙanana da masu matsakaicin ƙarfi na tsawon shekaru 150. A nahiyarmu wuraren da basu da masana'antu sune basu da ƙarfi sosai, domin rashin masana'antu na nufin yawan marasa aikin yi da rashin ababen more rayuwa, shi ya sa ƙarfin masana'antunmu ke da mahimmanci sosai"

Rikicin tattalin arzikin da ya afku a Turai ya yi tasiri a Jamus a shekarar 2009 amma ta gyagije da wuri bayan shekaru biyu, wannan ba abun mamaki ba ne kasancewar ita kanta Jamus ta taɓa kasancewa mafi talauci a duk nahiyar Turai. A shekarar 1998 Jamiyyar SPD da The Greens suka karɓi jagorancin gwamnati suka kuma ƙaddamar da Agendar sauye-sauye na 2010 wanda ya gyara yanayin samar da ayyukan yi da kuma tsarin kula da jin daɗin al'umma. A shekarar 2007 gwamnatin haɗakar jamiyyun CDU/CSU da SPD suka cigaba da waɗannan sauye-sauye inda suka ƙara shekarun yin retaya daga 65 zuwa 67. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi ƙarin bayani kan wannan batu.

Der SPD-Kanzlerkandidat Peer Steinbrück (l) unterhält sich am 11.06.2013 beim Tag der Deutschen Industrie in Berlin mit Ulrich Grillo (r), dem Präsidenten des Bundes der Deutschen Industrie (BDI). Foto: Tim Brakemeier/dpa
Ɗan takaran jami'yyar SPD Peer Steinbrück da shugaban ƙungiyar masu masana'antu Ulrich GrilloHoto: picture-alliance/dpa

Manufofin Jamus na daidaita tattalin arziƙinta

Mun kai wannan matakin ne saboda mun gudanar da sauye-sauye masu tsauri a yanayin samar da ayyukanmu a ƙasa mun kuma gudanar da sauyi a fanin zamantakewar al'umma ta fuskar tsaro muna amfani da agendar 2010

Duk da haka rikicin tattalin arziƙin ya bar baya da ƙura a fagen siyasar ƙasar. Ɗan takaran jamiyyar SPD mai adawa Peer Steinbrück yana jaddada cewa jamiyyarsa ta Social Demokrats a haɗakar gwamnatin na yanzu da jamiyya mai mulki CDU ce ke da alhakin yawancin matakan da suka daidaita matsalar kuɗi da samar da ayyukan yi a ƙasar. To sai dai jamiyyar adawa bata cin moriyar waɗannan sauye-sauye amma kuma ana danganta nasarar da aka yi wajen farfaɗo da komaɗar tattalin arziƙin Jamus da shugabar gwamnati Angela Merkel.

Rawar tattalin arziƙi a yaƙin neman zaɓe

A shekaru 10 da suka gabata idan aka tambayi kamfanonin Jamus abin da suke fuskanta sukan ce yawan albashi da kuɗin haraji da kuma yawan dogon turanci, waɗannan batutuwan da ƙyar ake maganansu yanzu, Steinbrück na neman a samar da mafi ƙarancin albashi amma Merkel ba ta amince da wannan ba. Sai dai kuma batun ƙarancin ƙwararrun ma'aikata da farashin albarkatu sun zo kan gaba a batutuwan da ake yi. Daga hasashen 'yan siyasa wannan na iya samun amsa lokacin yaƙin neman zaɓe.

An der JAGD auf FACHKRAEFTE beteiligen sich aus gehobener Position auf der Plattform eines Hubwagens Bundesarbeitsministerin Ursula von der LEYEN, Bundeswirtschaftsministetr Philipp ROESLER ( links neben v.d. Leyen) und der Vorstandsvorsitzende der Agentur fuer Arbeit, Frank-Juergen WEISE, rechts; die Aktion mit dem Riesenposter an der Front der Komischen Oper Unter den Linden sowie unterstuetzende Internetportale sollen helfen, den bis 2020 bestehenden Mangel an Fachpersonal von ca. 3 Millionen in den Griff zu bekommen am 05.06.2012 in Berlin.
Hoto: picture-alliance/dpa

Ga 'yan ƙasa da waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a batun adalci na da mahimmanci a gare su, yawancin mutane sun biya haraji saboda a ceto ƙasashe lokacin rikicin kuɗi domin ceto bankuna, kuma ko a wurin ayyuka, da yawa na ƙorafi kan rashin adalci, domin tsarin albashi da haraji sun yi hannun riga. To sai dai duk da waɗannan matsalo tattalin arziƙin Jamus na cigaba da ƙaruwa a dalilin haka ne ma ta zama abin koyi ga ƙasashen Turai.

Mawallafiya: Sabine Kinkartz/ Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal