1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattara sakamakon zaben jihohi ya yi nisa

Yusuf BalaApril 12, 2015

Baki daya abin da ake dako na zama sakamakon zaben gwamnonin jihohi 29 cikin 36 da kasar ke dasu da sakamakon 'yan majalisar dokokin jihohin.

https://p.dw.com/p/1F6bJ
Nigeria Präsidentschaftswahl 2015
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

A ranar Lahadinan ne ake fitar da sakamakon zaben gwamnonin jihohi a Najeriya bayan da al'umma suka kada kuri'unsu dan zabin wadanda zasu jagorancesu a matakin gwamna da 'yan majalisar jiha.

Baki daya abin da ake dako na zama sakamakon zaben gwamnoni jihohi 29 cikin 36 da kasar ke dasu da sakamakon 'yan majalisar dokokin jihohin. A lal misali a Kano an tattara sakamakon kananan hukumomi 34 a cikin 44 na jihar Kano kamar yadda wakilin DW Nasiru Salisu ya shaidar.

 

Gawamnoni dai na kasancewa masu karfin fada aji a matakan jiha har ma a wasu lokutan a matakan tarayya a kasar ta Najeriya da ke zama mai yawan jama'a kuma fitacciya a Afrika.

Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta Najeriya APC ta sa himma ne wajen ganin ta samu kari kan adadin gwamnoni da take dasu 14 bayan da a zaben shugaban kasa ta kafa tarihi da zabin Muhammad Buhari makwanni biyu da suka gabata, yayin da ita ma a nata bangaren jam'iyya mai mulki PDP ke duk mai yiwuwa wajen ganin ta rike kujerunta 21koma ta kara.

Hukumar zaben dai ta Najeriya a jiya Asabar ta bayyana gamsuwa da yadda zaben ya gudana duk da cewa an sami tashin tashina nan da can.