1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar Geneva ta tsaya cik

Yusuf BalaJune 17, 2015

Bangaren na 'yan Houthi sun ki fita tattaunawar da ake ci gaba da yi a Geneva a ranar Laraban nan bisa sanya idanun Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/1FilU
UN Genf Gespräche Jemen
Tattaunawar Majalisar Dinkin Duniya a Geneva kan makomar YemenHoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Shirin cimma sulhu tsakanin bangarori biyu masu gaba da juna a kasar Yemen na fuskantar barazana bayan da bangaren 'yan Houthi da ke zama 'yan Shi'a da Iran ke mara wa baya suka kaurace wa zaman tattaunawar da ake yi a Geneva karkashin sanya idanun Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar Reyad Yassin Abdullah da ke zama ministan harkokin wajen kasar ta Yemen babu wani ci gaba da aka samu, kuma ma ba shi da kwarin gwiwa kan cimma daidaito.

"Gaskiya ba ni da kwarin gwiwa akan wadan nan 'yan tawayen duba da irin munin aikinsu da kisan mutane da basu ji ba basu gani ba musamman a garuruwan Aden da Ta'iz da sauran biranen Yemen , kuma halayyar da suke nunawa tun da aka zo Geneva bata nuna alamun cewa suna da niyya ba a fahimci juna dan warware rikicin "

A cewar minista Abdullah 'yan tawayen na Houthi a ranar Laraban nan sun ki bayyana a wajen tattaunawar sun zauna a otel dinsu suna yada labarai marasa tushe.

A daya bangaren kuma wasu rahotanni sun nuna cewa wasu motoci makare da bama-bamai guda hudu sun tashi bayan tunkarar masallaci da hedikwar 'yan Houthi a birnin Sana'a, inda mutane da dama suka halaka.