1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Theresa May za ta fuskanci kuri'ar rashin amanna

January 16, 2019

Majalisar dokokin Birtaniya ta yi fatali da daftarin yarjejeniyar da Firaministar Theresa May ta cimma da kungiyar tarayyar Turai na ficewar kasar daga kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/3BcN6
England Brexit Theresa May
Hoto: Reuters TV

'Yan majalisar sun yi watsi da daftarin da gagarumin rinjaye a kuri’ar da suka kada a jiya inda yan majalisa 432 suka kada kuri’ar rashin amincewa yayin da yan majalisa 202 suka goyi bayan daftarin. Sakamkon da ke zama mafi muni cikin a cikin shekaru 95 da suka wuce.

Da ta ke jawabi bayan zaben Firaminista Theresa May ta yi bayani da cewa 

"Ta ce majalisa ta bayyana matsayinta kuma gwamnati za ta saurara, ta baiyana cewa majalisa ba ta goyi bayan wannan yarjejeniya ba, amma kuri’ar da aka kada bata nuna abin da ake goyon baya ba.“

Da yake mayar da martani shugaban Jam’iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya gabatar da bukatar kuda kuri’ar rashin amanna akan gwamnatin a yau Laraba, lamarin da zai iya jawo gudanar da zabe gabanin wa’adi.

"Yace wannan mummunan kaye ne ga wannan gwamnatin bayan shekaru biyu tana tattaunawar da ta gaza yin wani nasara, abin da ke gaban mu shine cewa gwamnati ta rasa amincin majalisa a kasar nan, a saboda haka ina gabatar da kudirin kada kuri’ar rashin amanna akan gwamnatin“.

Shugaban hukumar tarayyar Turai Jean Claude Juncker ya bukaci Birtaniya ta fayyace manufarta ba tare da wani jinkiri ba. Yana mai yin kashedin cewa ficewar kasar daga EU ba tare da cimma yarjejeniya ba zai yiwa kasar mummunan illa musamman wajen cinikayya da manyan abokan huldarta.