1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Thomas Duncan mai Ebola a Texas ya rasu

Pinado Abdu WabaOctober 8, 2014

Bayan mako daya yana jinya a asibiti, dan Liberiyan nan wanda aka gano da cutar Ebola a Amirka ya rasu. Gano shi da wannan cutar dai ya sanya fargaba a zukatan 'yan Amirka.

https://p.dw.com/p/1DSG9
Ebola Patient Thomas Eric Duncan verstorben 08.10.2014
Hoto: picture-alliance/AP/Wilmot Chayee

Dan Liberiyan nan da aka samu da cutar Ebola a Amirka ya rasu a asibitin da ya ke jinya a jihar Texas. Samun wannan mutumin mai suna Thomas Duncan da wannan cuta ne ya janyo hankalin jami'an kiwon lafiya, ga yaduwar wannan cuta a wajen nahiyar Afirka.

Kusan mutane 48 wadanda suka hadu da shi daga ranar da ya shiga kasar ranar 20 ga watan Satumba aka kebe, kuma bisa bayanan jami'an kiwon lafiya, kawo yanzu dai, duk cikinsu babu wanda ya nuna alamun cutar.

Ranar 25 ga watan Satumba ne ya je asibitin na Dallas a karon garko, inda aka sallame shi da magunguna, daga baya kuma aka maido shi asibiti a ranar 28 ga wata, kuma bincike ya nuna cewa yana dauke da cutar mai saurin kissa.

Kawo cutar Amirka da Duncan ya yi, ya sanya mahukuntan kasar inganta matakan yaki da cutar, abin da kuma ya sanya ayar tambaya kan sahihancin binciken da ake gudanarwa a filayen jiragen saman kasar.