1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Time: Merkel ce gwarzuwar shekarar 2015

Abdul-Raheem Hassan/ MABDecember 9, 2015

Mujallar Time ta yaba kokarin da Merkel ta Jamus ta yi a fannoni tattalin arziki da na jin kai a shekara ta 2015. Saboda haka ta zabeta a matsayin gwarzuwar 2015.

https://p.dw.com/p/1HKwL
Angela Merkel Person of the Year Time Magazine
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Time Magazine

Mujallar Time ta zabi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin gwarzuwar wannan shekara ta 2015, sakamakon rawar da ta taka a matsalar tattalin arzikin girka da kuma karbar 'yan gudun hijiran Syriya. Sannan kuma mujallar ta yaba gudunmawar da Merkel ta bada wajen daidaita tattalin arzikin kasashen Turai bayan da suka fuskanci matsalar komabayan tattalin arziki

A dangane da haka ne ma mataimakiyar Editan mujallar Time Radhika Jones ke ganin cancanci wannan karramawa.

"Gwarzuwar shekara ta 2015, Angela Merkel ta taka rawar gani a kasashen Turai, musamman wajen ceto tattalin arzikin wasu kasashen Turai dama batun bude iyayokin kasarta ga dubban 'yan gudun hijiran Syriya da ke neman mafaka a kasar a Jamus. Muna ganin wcewar adannan kudurori nata sun dauki hankalin duniya baki daya a baya-bayannan."

Ita dai Merkel mai shekaru 61 a duniya ta kasance mace ta hudu da mujallar Time ta taba zaba a matsayin gwarzon shekara, baya ga sarauniyar Ingila Elisabeth da kuma tsaohuwar shugabar Philippines Corazon Aquina.