1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu na APC ya lashe zaben shugaban kasa

March 1, 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya ta bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen mako.

https://p.dw.com/p/4O69F
Nigeria Wahl Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Sai dai tuni jam'iyyun adawa suka yi watsi da sakamakon zaben wanda aka yi tsammanin zai samar da sauyi wa kasar da ta fi ko wacce yawan al'umma a nahiyar Afirka.

A sakamakon wucin gadin da hukumar zabe ta INEC ta sanar, ta ce dan takaran na jam'iyya mai mulki ta APC ya tashi da da kuri'u miliyan 8.8 yayin da Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke biya mai da kuri'u miliyan 6.9 sai kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour wanda ya kusa yin ba-zata a matsayin na uku da kuri'u miliyan  6.1.

Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu shi ne da kansa ta bayyana sakamakon a gaban 'yan jarida da kimanin karfe 04:20 na wannan safiya agogon Najeriyar.

Idan an tabbatar da sakamakon na dindindin Bola Ahmed Tinubu mai shekaru 70 da haihuwa musulmi kuma dan kabilar Yarabawa, dan siyasa kuma tsohon gwamnan Legas shi ne zai gaji Shugaba Muhamadu Buhari da ke barin gado bayan share shekaru takwas a kan karagar mulki.

Sabon shugaban kasar dai na da manyan kalubale a gabansa wadanda suka hada da matsalar tsaro da kuma matsin tattalin arziki da ya jefa kasar cikin halin la'ilaha ula'i wanda ba ta taba fuskanta ba tun shekarar 1984.