1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton karuwar cin hanci da rashawa

January 28, 2021

Kungiyar Yaki da Rashawa ta Kasa da Kasa Transparency International, ta ce gwamnatoci na fakewa da annobar corona wajen nakasa kasashensu.

https://p.dw.com/p/3oXNa
BG "Die Welt im Griff von Corona"
COVID-19 ta janyo karuwar cin hanci da rashawaHoto: Tyrone Siu/REUTERS

Annobar dai na nufin dokar ta baci wadda ta shafi kowa da kowa. Tsawon shekara guda kenan gwamnatoci suka duka wajen taka rawa ta musamman, domin samar da mafita daga wannan yanayi ta hanyar samar da kayan da ake bukata a asibitoci da takunkumin kariya da allurar rigakafin corona da hanyoyin tallafawa al'umma da ma yadda za a rarraba wadannan kudaden. Sai dai ba nan gizo ke sakar ba a cewar Daniel Eriksson babban daraktan kungiyar Tranparency: "Babu gaskiya dangane da hanyoyin da wasu gwamnatoci ke bi wajen sayen kayayyakin kariyar jami'an kiwon lafiya da suka hadar da takunkumi da nau'rar taimakawa mutum numfashi da makamantansu. Hakan ya bai wa wasu damar azurta kawunansu ta wannan hanya, ba tare da la'akari da illolin da suke haifar wa ga al'umma ba, a takaice cin hanci na kisa."

Karin Bayani:Bankado badakalar cin hanci a harkar mai a Nijar

Kungiyar ta Tranparency International dai, ta yi kaurin suna wajen yaki da cin hanci da rashwa a fadin duniya. A kowace shekara, ta kan yi nazarin halin da  kasashe ke ciki a fannin cin hanci da almundahana da dukiyar kasa da rashin gaskiya. Baya ga haka ta kan kuma duba matsayin dokokin yaki da matsaloli da kuma yiwuwar amfani da ita, abin da ya shafi shekarar corona ta 2020.

Mobiles Impf-Team in Potsdam Coronavirus
Fakewa da corona domin azurta kaiHoto: Tessa Walther/DW

Binciken da kwararru suka gudanar dai, na nuni da cewar duk da wannan hali na ni 'yasu da duniya ta tsinci kanta a ciki, maimakon sauki sai ma ta'azzara rashawa ta kara yi tsakanin kaso biyu daga cikin 180 da aka yi nazari a kansu. Denmark da New Zealand su ne a jerin kasa, inda cin hancin bai yi yawa ba, sai Finland da Singapore da Sweden da kuma Switzerland, a yayin da Jamus ta ke a matsayi na takwas. Daniel Eriksson ya yi tsokaci: "Hakan ba ya nufin cewar kasashen da sunayensu yake sama ba sa fama da rashawa. Suna fuskantar rashawa a bangaren ayyukan gwamnati. Kuma wasu daga cikin kasashen da ke jerin farko, su ne ke taimakawa wajen assasa rashawa a kasashen da sunayensu ke kasa."

Karin Bayani:Matsayin Najeriya a cin hanci da rashawar duniya

Rahoton bai fayyace matsayin Somaliya da Afirka ta Kudu ba. A cewar kungiyar dai a wadannan kasashen ne aka fi tabka rashawa, sai kuma Venezuela da Yemen da Siriya. Sakamakon binciken na Tranparency dai, ya nunar da cewar matsalar cin hanci da karbar rashawa ta fi muni a kasashen da ke yankin Kudu da Saharar Afirka. Kasashen yammaci na tsaka-tsaki. Da irin wannan kididdiga da ke bayyana matsayin kasashe, kungiyar ta Transparency na kokarin kara bayyana matsalar rashawa da nufin kara matsin lamba a kan kasashen da matsalar ta fi yi wa katutu.