1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta sa Trump ya dage taron G7

Mouhamadou Awal Balarabe
March 20, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ne ya kamata ya karbi bakuncin taron na G7 a watan Yuni, amma barazanar da annobar corona ke yi ya sa shi sauya salon gudanar da taron, inda maimakon haduwa za a tattauna ta kafar bidiyo.

https://p.dw.com/p/3ZmRN
Frankreich G7 Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm

Gwamnatin Amirka ta soke taron koli na shugabannin kasashe da suka fi karfin masana'antu a duniya wato G7 da ya kamata a gudanar a Camp David a watan Yuni saboda barkewar cutar Corona. Sai dai fadar mulkin ta White house ta ce maimakon taron keke da keke, shugabannin kasashe da gwamnatoci bakwan za su yi amfani da kafar bidiyo wajen yin musayar yawu tsakaninsu . 


Kasashen da aka fi ji da su a fannin tattalin arziki a duniya wadanda suka hada da Birtaniya da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Amirka suna haduwa sau daya a kowace shekara don tattaunawa kan muhimman kalubale da ake fuskanta. A wannan shekara dai, shugaban Amirka Donald Trump ne ya kamata ya karbi bakuncin taron na G7.