1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya yi amai ya lashe kan Rasha

Abdul-raheem Hassan MNA
July 18, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya sauya kalamansa na wanke Shugaba Putin daga zargin kutse da cewa ya yarda da zargin da hukumar leken asirin Amirka ke yi wa Mosko da yin shishshigi a zaben 2016.

https://p.dw.com/p/31dIM
USA, Washington: Trump kommentiert das Treffen mit Putin im US-Kongress
Hoto: picture-alliance/O. Douliery

A wani yunkuri na kwaskware subutar baki a yayin ganawarsa ta musamman da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Helsinki na kasar Finlan, Shugaba Donald Trump Amirka ya ce kuskure ne a kalamansa na farko da ya fifita Rasha a kan hukumar tattara bayanan sirrin Amirka na zargin taimaka wa Trump a kan Hillary Clinton a zaben shekarar 2016.

Trump ya lashe aman da ya yi ne kwana guda bayan da ya sha suka daga 'yan majalisar Amirka ciki har da 'yan jam'iyyarsa ta Republican da suka bukace shi ya sauya matsayinsa cikin gaggawa.