1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsarin kiwon lafiya ga kowa a Najeriya

March 12, 2014

Mahukuntan kasar sun kaddamar da wani sabon shirin wata inshorar lafiya da za ta taimaka wajen rage tasirin cututtuka da ake fama dasu a cikin Najeriyar.

https://p.dw.com/p/1BOet
Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Ta dai kai ga cirar tuta ga batun mutuwar mata da yara kanana a tsakanin 'yan uwanta da ke sassa daban daban na duniya, to sai dai kuma tana shirin sauyawa ga Najeriya da ta kaddamar da sabon shirin tabbatar da lafiya mai inganci a tsakanin kowa.

Karkashin sabon shirin da muhukuntan kasar ke fatan kaiwa ga shiga birane da karkarar kasar dai, duk wani mai buga wayar salula zai biya haraji na musamman domin batun na lafiya, a yayin kuma da mai shiga jirgin sama ma zai biya nasa harajin da gwamnatin ta ce za ta tara ta kai ga ginin asibitoci da samar da magunguna kyauta ga tsofaffi da mata da yara, a yayin kuma da masu karfi a jiki za su biya kadan a fadar Dr Ado Mohammed dake zaman shugaban hukumar matakin farko na lafiyar kasar da kuma ya kara bayanin yanda shirin zai kai ga gudana.

"Kamar wadanda suka gaji, tsofaffi da yara da mata masu juna biyu, gwamnati za ta kula dasu. Amma masu karfi akwai wani shiri da a cikinsa za'a hada kudi kamar naira 150 a duk wata wanda za ku kafa kungiya ku rika biyan wannan adadi kuna bai wa wanda ke kula da lafiyar ku. Wannan ma shi ne yafi tasiri fiye da abun da gwamnati za ta yi".

Nigeria Abuja Maitama Hospital Krankenhaus Unterernährung
Hoto: DW

Da kobo kobo dai kasar ta Najeriya na fatan ninka yawan kudin da kasar ke iya kashewa da misalin kaso 500 cikin 100 a duk shekara, abun kuma da ko bayan wadatar da magunguna da sauran harkoki na lafiya a matakai daban daban, ke nufin tallafin talakawan kasar wajen rayuwa ta gari, a cewar Dr Khaliru Hassan da ke zaman karamin ministan lafiyar kasar ta Najeriya.

"Mutane da yawa na wahala kwarai wajen samun magani, saboda haka aka ga ya kamata a kara fadada taimakon da ake ba mutane. Taimakon zai fito ne daga gwamnati da kuma kansu mutanen anyi tarbace ne domin a samu ci gaba".

Sabon shirin dai a karon farko, na fatan kowane dan kasar zai biya 'yan kudi kadan tare da samun tallafi daga jihohi da ma gwamnatoci na kananan hukumoni wajen tallabar batun na lafiya,

Tallafin kuma da a cewar Ibrahim Hassan Dan Kwambo da ke zaman gwamnan jihar Gombe, ke iya dogara ga nasarar shirin a matakin farko na lafiya.

"Kamar riga-kafi da sauran magunguna da kuma haihuwa da shawara da sauransu, in muka ingantasu kamar Gombe muka samu mutane suna yi to zai zamo mataki na inganta wannan niyya ta gwamnati wajen samar da lafiya cikin sauki".

Nigeria Abuja Maitama Hospital Krankenhaus Schwester Harriet
Hoto: DW

To sai dai in har tana shirin yin kyau a matakin farko na lafiyar a jihar Gombe, ga 'yar uwarta ta Borno da ke fama da rigingimu dai, daga dukkan alamu har yanzu akwai sauran tafiya duk da tallafin, a fadar kwamishinar lafiyar jihar, Salma Anas Kolo da ta ce tuni an kai ga lalata daukacin bukatun na matakin farko sakamakon hari na 'yan kungiyar ta Boko haram;

"Wannan abu da ake ciki ya shafi lafiya amma bai kai ga tsaida cigaba ba , muna da kananan asibitoci kusan 20 da aka kona, yawanci kuma a kananan hukumomi, musamman ma kayan riga-kafin yara, saboda munyi ta ja-munyi ta ja kan harkar Polio sannan kuma da magungunan da ake bayarwa don dakatar da haihuwa."

Abun jira a gani dai, na zaman nasarar shirin cikin kasar ta Najeriya da ke fuskantar sashen lafiyar da ke nuna alamun gajiyawa yanzu.

Mawallafi: Ubale Musa

Ediat : Saleh Umar Saleh