1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karuwar hare-hare a shiyyar Arewa maso Gabas

June 4, 2020

Harkokin tsaro na kara tabarbarewa a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya inda mayakan Boko haram ke zafafa hare-haren da su ke kaiwa a sassan jihar Borno tare kame mutane su yi garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/3dGwE
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Harkokin tsaro na kara tabarbarewa a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya inda mayakan Boko haram ke zafafa hare-haren da su ke kaiwa a sassan jihar Borno tare kame mutane su yi garkuwa da su.


Na baya bayan nan shi ne wanda mayakan na Boko haram suka sake kame wasu sojoji da masu aikin jin kai guda uku yayin da su ke tafiya a kan babar hanyar Maiduguri zuwa Munguno inda suke gudanar da ayyukansu na jin kai.
Ko a ranar Talatar da ta gabata mayakan Boko Haram sun hallaka kimanin mutane shida tare da jikkata wasu da dama a wasu jerin hare-haren da suka kai a wasu sassan Jihar Borno, lamarin da kuma ya tilasta daruruwan mutane guduwa daga gidajensu zuwa tsaunika da wasu garuruwa don tsira da rayukansu.


Daga cikin garuruwan da lamarin ya ritsa da su har da Kwabula da ke da nisan kilomita shida daga Jakana a Karamar Hukumar Konduga inda suka bude wuta na kan mai uwa da wabi nan take suka hallaka mutune hudu tare da jikkata wasu da dama. Kazalika mayakan sun kai hari a kauyen Khaddamaru da ke karamar hukumar Jere inda nan ma suka hallaka mutum daya tare da jikata wasu da dama tare da kwashe wasu muhimman kayayyakin yaki na sojojin Najeriya da kuma kona sabuwar sakatariyar karamar hukumar. Sai kuma harin bam da aka aje a sansanin ‘yan gudun hijira na Farm Center da ke Maiduguri, bam din da wani yaro ya dauka yana wasa sai ya tashi da shi ya hallaka iyayensa da ke kusa suka jikkata.

Nigeria Selbstmordanschlag in Maiduguri ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/Str


Sai kuma kame wasu sojoji da masu aikin jin kai da mayakan Boko Haram suka yi a kan hanyar Maiduguri zuwa Munguno abin da ya tada hankluam al’umma ganin ko a watanni baya mayakan na Boko Haram sun hallaka ma’aikatan jin kai da suka kame. Wannan na kara jefa ayyukan jin kai cikin mawuyacin hali da ya sa ma’aikatan jin kai guje wa ayyukansu na taimaka wa al’umma kamar yadda Junaidu Usman mai aikin agaji a yankin Munguno ya tabbatar. Yanzu haka dai jama’a na ci gaba da bayyana fargaba kan yanayin tsaro musamman a sassan jihar Borno inda su ke neman agajin gaggawa da hukumomi.

Nigeria Armee Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

Yanzu haka dai ana ci gaba da shawatar gwamnati kan hanyoyin da za a bi a magance wannna matsalar tsaro da aka kwashe sama da shekaru goma ana fama da ita. Ya zuwa yanzu dai hukumomi ba su ce komai kan wadannan hare-hare ba amma dai a wata sanarwa da Rundunar Sojojin Najeriya ta fitar ta nuna cewa sojojin na samun galaba har ma da hallaka wasu manyan kwamandoji da ke bangaren Abubakar Shekau.