1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta tsaurara matakan tsaro

January 10, 2015

Ministan harkokin cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve ya bayyana cewa ana ci gaba da tsaurara matakan tsaro a kasar bayan da wasu 'yan ta'adda suka hallaka mutane 17 a wasu hare-hare biyu da suka kaddamar.

https://p.dw.com/p/1EIL9
Hoto: Reuters/Y. Boudlal

Cazeneuve ya bayyana hakan ne bayan kammala wani taron gaggawa da ministocin kasar suka gudanar a yau Asabar a fadar gwamnatin kasar ta Elysee. Taron na su dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da jami'an 'yan sanda ke ci gaba da farautar mutum ta hudu da ake zargi da kai harin da ta kasance mace bayan da suka samu nasarar kashe uku daga cikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron sun yi gargadin cewar matar na dauke da muggan makamai kuma tana da hadarin gaske. Kawo yanzu dai jami'an tsaron Faransan na tsare da wasu mutane 16 da ake zargi da hannu a harin, wadanda ya hadar da wanda aka kai a ofishin wata mujalla mai zanen barkwanci.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo