Tsohon jami'in lafiya ya halaka mutane 100 a Jamus
October 30, 2018Talla
Alkali mai shari'a a arewacin birnin Oldenburg Sebastian Buehrmann ya tambayi Niels Hoegel ko ya amince da zarge-zargen da ake masa na kisan marasa lafiyar? Sai ya ce "haka ne abin da ya aikata kenan" kamar yadda Hoegel dan shekaru 41 ya bayyana a gaban kotu.Tshohon ma'aikacin jinyar dai ya rika ba da magunguna fiye da kima ga marasa lafiyar.
Mai gabatar da karar ya ce babban burin bude sauraren karar shi ne samar da haske cikin duhu kan irin ta'asar da ta dauki lokaci ana aikatawa a wasu asibitoci biyu na kasar ta Jamus don kaucewa gaba.