1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da al’ummar da suka bace

Kamaluddeen Sani Shawai RGB
August 30, 2017

Ranar 30 ga watan Agusta na kowacce shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin tunawa da mutanen da aka tilastawa bacewa daga cikin al’umma a sakamakon zalunci ko yake-yake.

https://p.dw.com/p/2j668
Mexiko - Proteste gegen das Verschwinden von 43 Studenten
Hoto: picture-alliance/dpa/JMA

An gudanar da taron karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya domin tunawa da mutanen da aka tilastawa bace wa daga cikin al'umma a sakamakon zalunci ko yake-yake wanda hakan ne ya sanya kungiyoyi gami da hadin gwiwar hadaddiyar majalisar kungiyoyin mata a Najeriya shirya taro na musamman domin wayar da kan jama'a bisa mahimmacin da ke tattare da ranar tare da daukar matakan dakile matsalolin.Taron na bana wanda ya hada kan kungiyoyi masu fafutukar kare ‘yancin bil Adama da cibiyoyin bunkasa ci gaban al'uma da wakilai daga bangarorin gwamnati da kungiyoyin masu zaman kansu duk domin raya ranar da Majalisar ta Dinkin Duniya ta ware don waiwaye kan kalubalen da bil Adama ke fuskanta sakamakon tilasta musu bacewa.

Daliliai masu tarin yawa da suka kun shi yake-yake ko cin hanci da rashawa da gallazawa da mafi yawanci ya fi shafar mata da kananan yara a tarayyar Najeriya kamar sauran kasashen duniya  da ke fuskantar irin wadannan matsalolin. A karshen taron dai cibiyoyin da suka fito daga sassa daban na Najeriya sun bayyana cewar kamata ya yi a dauki matakai masu tsauri domin hukunta wadanda ke aikata wadannan laifuffukan gami da karfafa gwiyoyin mata ta fuskar nema masu ilimi da bayanai ganin akasari su ne su ke fuskantar wadannan matsaloli na tilasta musu barin yankunan su a yayin barkewar rikici.