1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya na adawa da kawancan Amirka da Kurdawan Siriya

Gazali Abdou Tasawa
May 17, 2017

Shugaba Erdogan da ke ziyara a Amirka ya bayyana wa Shugaba Trump rashin amincewarsa da kawancan da Amirka ke yi da mayakan Kurdawan Siriya a yaki da IS.

https://p.dw.com/p/2d59u
Erdogan und Trump USA
Hoto: Reuters/K.Lamarque

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya gana da shugaba Trump na Amirka inda ya soma wata ziyarar aiki. Batun kawancan da Amirka ke yi da mayakan kurdawa Siriya a yaki da Kungiyar IS da kuma na Fetullah Güllen shahararren malamin nan dan asalin kasar ta Turkiyya da hukumomin Turkiyar ke nema ruwa a jallo, da amma kuma ke samun mafaka a Amirka, na daga cikin muhimman batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna. 

Tuni dai Shugaba Erdogan ya bayyana wa Shugaba Trump rashin amincewarsa da yadda Amirkar ke taimaka wa mayakan Kurdawan  Siriya. Sai dai Shugabannin kasashen biyu mambobin kungiyar kawancen tsaro ta NATO ko OTAN wadanda kuma ke yabawa juna sun sha alwashin samun fahimtar juna a tsakaninsu.

Sai dai lokacin isar Shugaba Erdogan a birnin Washington daruruwan magoya bayan Kurdawa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawarsu da shugaban. Kuma mutane tara sun jikkata kana aka kama biyu a lokacin dauki-ba-dadin da suka yi da jami'an da ke  tsaron lafiyar shugaba Erdogan.