1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya na janye sojoji daga Iraki

Kamaluddeen SaniDecember 14, 2015

Turkiya ta fara janye sojojin ta da ke a wani sansani a birnin Mosul na arewacin Iraki a wani matakin warware kiki-kaka da ta dabaibaye zaman sojojin Turkiya a Iraki.

https://p.dw.com/p/1HNGv
Türkei Armee Soldaten Symbolbild
Hoto: picture-alliance/AA/V. Gurgah

A yayin mayar da martani kan matakin da Turkiyan ta dauka Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier yayi nuni da cewar:

Yau mun ga alamun farko a inda Turkiya ta bayyana janye sojoji daga Iraki, Ina fata hakan zai kawo karshen zaman yanayin dardar a daukacin yankin, ba za kuma mu amince da wani rikici a yankin ba.

A wannan watan ne dai Iraki ta nuna rashin jin dadi bayan da Turkiyan ta jibge sojoji 150 gami da wasu tankokin yaki 25 a kusa da Mosul wanda ya sanya kasashen Amirka da Jamus daukar wani matakin sasanta takaddamar domin hada hannu wuri guda domin yakar kungiyar IS.