1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta soki lamirin EU

Kamaluddeen SaniMarch 7, 2016

Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya soki lamirin kungiyar EU bisa gazawar wajen basu tallafin kudaden da suka yi alkawari don takaita kwararar 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1I8sS
Türkei Anschlag in Ankara - Präsident Recep Erdogan
Hoto: picture-alliance/dpa/Turkish President Press Office

A yayin jawabin sa ga a gaban shugabanin kungiyar a yau a Brussels, Erdogan ya ce kungiyar har yanzu ta kasa cika alkawarin da ta dauka na bata tallafin Euro biliyan uku a inda ya kara da cewar ya na saran firiministan kasar ya komo gida da kudaden da aka yi musu alakawarin.

Kazalika shugaban Turkiyan ya kuma yi kakkausar suka ga kungiyar Turan na rashin nuna katabus wajen karbar 'yan gudun hijira gami da neman Turkiyan hana kwararar 'yan gudun hijirar.

Shugaban ya kara da cewar ''ba mu ne muke tura su ba su ne suka ga damar yin tattakin zuwa kasar Girka a yayin da mafi yawansu ke mutuwa a hannu daya kuma an sami nasarar ceto rayuka sama da dubu goma daga teku.''